Dosso (birni)

Yanki ne na wasu al'ummar ƙasar Nijar

Dosso birni ne dake kan kwanar kudu maso yammacin kasar Nijar. Birnin na tsakanin kilomita 130 - 140 (mil 81-87) kudu maso gabashin babban birnin kasar wato Niamey a kan marabar hanyar zuwa birnin Zinder kasar Benin. Birni na bakwai mafi yawan jama'a a kasar ta Nijar kuma mafi girma a yankin gundumar Dosso, a kidayar shekarar 2001 akwai mutane kimanin 43,561. Birnin ne cibiyar gundumar wanda kuma ya kunshi bangarorin gudanarwa guda biyar dake kudu maso yammacun kadar Nijar.

Dosso


Wuri
Map
 13°03′N 3°12′E / 13.05°N 3.2°E / 13.05; 3.2
JamhuriyaNijar
Yankin NijarYankin Dosso
Department of Niger (en) FassaraDosso
Babban birnin
Yawan mutane
Faɗi 58,671 (2012)
Labarin ƙasa
Altitude (en) Fassara 227 m
Bayanan tarihi
Ƙirƙira 1750
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci

Tarihi gyara sashe

 
Hoton Baoura, a gidan Tarihi na Dosso, Nijar

Masrautar Dosso na zaunene a garin na Dosso, Kafin shigowar turawan mulkin mallaka masarautar Zarma ce ta mamaye dukkan yankunan na Zarma. Sarkin gargajiyar yankin ana kiran sa da Zarmakoy ko Djermakoy na Dosso. Ma'ana Sarkin Zarma ko (Djerma).

Muhallai gyara sashe

Manyan muhallan birnun akwai Masarautar Djermakoy da gidan ajiye kayan tarihi wanda yake daga cikin guwaren abubuwan mamaku na Majalisar dinkin duniya wato UNESCO World Heritage Sites a 2006.

Sufuri gyara sashe

Birnin na Dosso mahadar kasuwanci ne na shiga da fitar kaya daga birnin Kwatano na kasar Benin. Sakamakon shigo da kaya zuwa birnin Niamey ne Dosso ta zama matattarar sufuri na kanana da manyan motoci. Akwai hanyar jirgin kasa dake kan aiki a halin yanzu.

A wani ƙari kuma akwai shirin gina tashar sauke kaya ta doron kasa.

Sanannun mazauna birnin gyara sashe

  • Rabiou Guero Gao - Dan wasan tsere na dogon zango a kasar Nijar.
  • Zakari Gourouza - Dan wasan Olympic na kasar Nijar

Hotuna gyara sashe

Manazarta gyara sashe