Domitille Barancira
Domitille Barancira Alkaliya ce, 'yar kasar Burundi wadda ta jagoranci kotun tsarin mulki daga shekarar 1998 zuwa 2006. Daga baya ta zama jakadiyar Burundi a Jamus.
Domitille Barancira | |||||
---|---|---|---|---|---|
2007 - 2010
1998 - 2006 | |||||
Rayuwa | |||||
ƙasa | Burundi | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | mai shari'a da Mai wanzar da zaman lafiya |
Aiki
gyara sasheDomitille Barancira ta yi digirin a fannin shari'a a Jami'ar Burundi.Ta yi aiki a matsayin alkali tsakanin 1983 zuwa 1996, inda ta zama mataimakiyar shugaban kotun koli daga 1992 zuwa 1996. Ta kasance shugabar kotun daukaka kara ta Bujumbura na tsawon shekaru biyu sannan ta zama shugabar kotun tsarin mulki a shekarar 1998. Shugaba Pierre Buyoya ne ya nada ta a wannan mukami kuma ta rike ta har zuwa shekara ta 2006. Ta kuma kasance shugabar hukumar gyara da sabunta tsarin shari'ar Burundi.[1] A shekara ta 2006, ta kasance ‘yar takarar Kotun Afirka akan ‘Yancin Dan Adam da Jama’a.
A shekara ta 1997, Barancira ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Faransa cewa, mutane 17 da aka yanke wa hukuncin kisa sakamakon rikicin kabilanci bayan kisan da aka yi wa Shugaba Melchior Ndadaye a 1993, sun daukaka kara kan hukuncin da aka yanke musu ba tare da yin nasara ba. Ta kara da cewa babu wanda aka yankewa hukuncin kisa tun shekaru 15 da suka gabata na cin naman mutane. A cikin kotun daukaka kara, ta tabbatar da hukuncin kisa ga Pierre Nkurunziza a shekarar 1998; Daga baya ta samu rantsuwar sa a matsayin shugaban kasa a shekara ta 2005, lokacin da ta kasance shugabar kotun tsarin mulkin kasar. A cikin shekarun 2000, ta zama daya daga cikin masu fafutukar kare hakkin mata a Burundi tare da Catherine Mabobori, Vestine Mbundagu, Marie-Christine Ntagwirumugara da Sabine Sabimbona. A 2007, ta zama jakadiyar Burundi a Jamus; ta yi ritaya daga mukamin a shekarar 2010.
Manazarta
gyara sashe- ↑ Cite error: Invalid
<ref>
tag; no text was provided for refs namedWL