Domingas Togna
Domingas Embana Togna (an haife ta a ranar 14 ga watan Yuni, 1981) 'yar wasan tsere ce daga Guinea-Bissau.[1]
Ta yi gasar tseren gudun fanfalaki a gasar cin kofin duniya ta shekarar 2007, ba tare da ta gama ba,[2] sannan a cikin tseren mita 1500 a gasar Olympics ta 2008, ta kammala a matsayi na goma sha ɗaya a cikin heat [3] da na 33 gaba ɗaya.[4]