Dmytro Dikusar
Dmytro Petrovych Dikusar (Oktoba 24, 1985, Odesa, Ukraine SSR, Tarayyar Soviet ) ɗan rawa ne kuma ɗan mawaki na kasar Ukraine.[1]
Dmytro Dikusar | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Odesa (en) , 24 Oktoba 1985 (39 shekaru) |
ƙasa | Ukraniya |
Sana'a | |
Sana'a | mai rawa da Mai tsara rayeraye |
Tarihin Rayuwa
gyara sasheAn haifi Dmytro Dikusar a ranar 24 ga watan Oktoban 1985 a Odesa. Ya fara rawa tun yana dan shekara 6, da farko a dakin rawa, sannan daga baya a wurin wasanni.[2]
Ya sami ilimi na babban mataki a Kyiv Institute of Physical Education, a shekara ta 2008 ya sami takardar shaidar difloma a matsayin mai horar da rawa. Dmytro ya halarci wasanni da aka gudanar a Ukraine da kuma gasar kasa da kasa na tsawon shekaru masu yawa. Ya samu babbar nasara a raye-rayen Latin Amurka - ya kai wasan karshe a gasar cin kofin Turai, kuma shi ne ya lashe gasar cin kofin duniya a irin wannan salon rawa.
A shekarar 2006, Dmytro Dikusar ya samu lakabi na dan takarar Mastan wasanni (master of sports) a rawa ballroom. Ya sha kai wasan karshe na gasar kasa da kasa da gasar zakarun kasar Ukraine.
Ya samu karbuwa a kafafen watsa labarai a 2007 bayan da ya taka rawa a karo na biyu na kakar gasar "Rawa tare da Taurari - Dancing with the Stars" a gidan TV tashar "1 + 1".[3] Ya yi rawa tare da mawaƙiya Iryna Bilyk. Daga baya, sun fara soyayya, kuma ba da daɗewa ba suka yi aure, sun gudanar da wani babban biki a Rio de Janeiro. Duk da haka, a cikin 2010, ma'auratan sun rabu.
A 2011, ya shiga gasar Rasha "Rawa tare da taurari". Bayan haka, ya kuma yi aiki tare da sigar Georgian na wannan wasan kwaikwayo.
A cikin 2012, Dmytro ya fara dangantaka da 'yar rawa Olena Shoptenko, wanda yahadu da ita wa wajen gasar Rawa tare da Taurari. A 2013, ma'auratan sun yi aure. Amma ko da wannan auren bai daɗe ba - a cikin 2016, ma'aurata sun rabu.[4]
A shekarar 2019, ya koma wasan kwaikwayo na "Rawa tare da Taurari".[5] A cikin yanayi na shida, bakwai da takwas, ya yi rawa bi-biyu tare da Victoria Bulitko, Slava Kaminska da Olga Harlan, bi da bi.[6]
A cikin 2022, ya shiga aikin Soja don kare Ukraine a lokacin harin Rasha[7]
Nassoshi
gyara sashe- ↑ "Dmitry Dikusar". Obozrevatel.
- ↑ "Facts about Dikusar". 1+1 TV Channel.
- ↑ "Noone owns anything". Archived from the original on 2022-04-12. Retrieved 2023-03-28.CS1 maint: BOT: original-url status unknown (link)
- ↑ "Дмитро Дікусар про болісний розрив з Шоптенко: "Я кохав довго і сильно"". Archived from the original on 2022-04-04. Retrieved 2023-03-28.CS1 maint: BOT: original-url status unknown (link)
- ↑ "Dancing with the stars". Archived from the original on 2022-04-04. Retrieved 2023-03-28.CS1 maint: BOT: original-url status unknown (link)
- ↑ "Dancing with the stars". Archived from the original on 2022-04-04. Retrieved 2023-03-28.CS1 maint: BOT: original-url status unknown (link)
- ↑ "For the first time in three months: choreographer Dmytro Dikusar spoke from the front line". Unian.