Didas Kayihura Muganga
Kayihura Muganga Didace lauya ne ɗan ƙasar Rwanda kuma masani. Tun daga watan Yuli 2022, yana aiki a matsayin Mataimakin Mataimakin Shugaban Jami'ar Ruwanda.[1][2]
Didas Kayihura Muganga | |
---|---|
Rayuwa | |
ƙasa | Ruwanda |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar Rwanda |
Sana'a | |
Sana'a | Malami da Lauya |
Ilimi
gyara sasheKayihura Muganga Didace ya karanci shari'a a tsohuwar jami'ar ƙasar Rwanda. Yana da digiri na biyu a fannin shari'ar kasuwanci ta duniya daga Jami'ar Utrecht.[3] A shekarar 2015, ya kammala digirin digirgir (Ph.D). daga Jami'ar Utrecht. Ph.D. bincike mai suna (Corporate Governance and the liability of Corporate Directors: The case of Rwanda).[4]
Sana'a
gyara sasheKayihura shi ne tsohon shugaban riko na Kwalejin Fasaha da Kimiyyar Jama'a ta Jami'ar Rwanda (CASS). Ya yi aiki a matsayin Rector na Institute for Legal Practice and Development (ILPD) daga shekarun 2016 zuwa 2017. Bugu da kari, Ya yi aiki a matsayin shugaban tsangayar shari'a ta Jami'ar Ƙasa ta Ruwanda (UR) (2007-2009).[5][6]
Bugu da kari, Kayihura shi ma mai sharhi ne kan harkokin shari'a kuma mai yin shawarwari.[5]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "University of Rwanda". ur.ac.rw (in Faransanci). Retrieved 2023-06-19.
- ↑ Favour, Esther (2022-07-16). "Kagame appoints new leaders for University of Rwanda". The New Times (in Turanci). Retrieved 2023-06-19.
- ↑ "DR. DIDAS M. KAYIHURA - Directory". findlaw.africa (in Turanci). Retrieved 2023-06-19.
2015 His PhD research was on “Corporate Governance and the liability of Corporate Directors: The case of Rwanda”; PhD from Utrecht University – The Netherlands. Master’s Degree (LL M)-International Business Law from Utrecht University (2006); Bachelor’s Degree (LL B/Hons) from the National University of Rwanda
- ↑ "CORPORATE GOVERNANCE AND THE LIABILITY OF CORPORATE DIRECTORS: THE CASE OF RWANDA" (PDF).
- ↑ 5.0 5.1 Buningwire, Williams (2022-07-16). "Who is Dr. Didas Kayihura, The New Vice Chancellor Of University Of Rwanda?". KT PRESS (in Turanci). Retrieved 2023-06-19.
- ↑ "Dr Didas Kayihura Muganga yagizwe Umuyobozi w'agateganyo wa Kaminuza y'u Rwanda".