Dashishi abincin gargajiya ne da ke kara lafiya da kuzari tare da gina jiki, ga shi kuma da dadin gaske.

Kayan da ake bukata:

gyara sashe
  • Alkama kofi 8
  • Mai kofi 1
  • Gishiri kadan
  • Ruwa

Yadda ake yi:

gyara sashe
  1. Ki sami alkama ki tsince ta sai a surfeta a cire dusar.
  2. A wanke ta, a bari ta bushe, sai a nika a barzo ta amma kada ta yi gari sosai.
  3. A zuba ruwa a tsame ta yadda barjin zai yi laushi idan an turara shi, sai a tsame.
  4. A sami madanbaci a turara shi, har sai ya fara cuccurewa,
  5. Daga nan sai a zuba mai da gishiri a juya sosai amma a sauke.
  6. Sai a sa mai yadda zai warware, a kara mayarwa shi kan wuta.
  7. Idan ya yi za a ji yana kamshi, sai ci.

Ana ci da miyar taushe ko miyar ganye ko duk miyar da ake so.