Danbun masara abincine na gargajiya mai dadin gaske

Kayan Hadin danbun masara

gyara sashe

1.masara

2.zogale

3.attarugu da albasa

4.kori da kuma danyar citta

5.sinadarin dandano

6.man gyada

7.gyada

8.kifi

Yanda ake hadashi

gyara sashe

Abu na farko da zaki fara yi shine ki gyara masaranki ki kaita barji amma kananan barji ba manyaba idan ankawomiki sai ki tankadeshi ki wanke tsakinki sai ki dora tukunyar dambunki ki zuba tsakinki sai kisa leda ki rufe idan yadahu sai ki saukeshi ki zubashi acikin roba sai ki kuma wankehi ki matseshi sannan sai ki barbazashi kisanya kayan hadinki sai kimaidashi acikin tukunyarki idan yadahu sai ki saukeshi kisa manki dambunki ya kammala.