dan malele wani nau'in abinci ne daga masara, da farko za'a kai masara gurin mai nika ya barza, sai a kawo gida a tankade, idan aka tankade, sai ayi amfani da tsakin a wanke shi, a dora tukunya akan wuta a zuba ruwa a ciki a rufe, idan ya tafasa sai a dauko wannan tsakin da aka wanke a zuba a cikin tukunyan anayi ana juya wa kar yayi guda, idan yayi kauri sai a sauke a juye a faranti a barshi ya sha iska, sai a barbada yaji da maggi da manja, sai ci.