Dame Virginia Ngozi
Dame Virginia Ngozi Etiaba, CON. (an haife ta ranar 11 ga watan Nuwamba, 1942). Tsohuwar Gwamniyar Jihar Anambra, dake kudu maso gabashin Nijeriya ce, daga Nuwamba shekarar 2006 zuwa Fabrairu 2007. hakan yasa ta zama mace ta farko a tarihin Najeriya da ta zama gwamna. An sanya ta ne yayin da majalisar dokokin jihar ta tsige gwamnan da ya gabata, Peter Obi saboda zargin rashin ɗa'a. Ta mayar da ikonta ga Obi watanni uku bayan haka lokacin da kotun daukaka kara ta soke tsigewar.[1]
![]() | |||
---|---|---|---|
3 Nuwamba, 2006 - 9 ga Faburairu, 2007 ← Peter Obi - Peter Obi → | |||
Rayuwa | |||
Cikakken suna | Virginia Ngozi Etiaba | ||
Haihuwa | Nnewi, 11 Nuwamba, 1942 (82 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Ƙabila | Tarihin Mutanen Ibo | ||
Harshen uwa | Harshen, Ibo | ||
Karatu | |||
Harsuna |
Turanci Harshen, Ibo Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Kyaututtuka |
gani
|
Asali
gyara sasheEtiaba yar asalin Ezekwuabor Otolo-Nnewi ne a karamar hukumar Nnewi ta Arewa a jihar Anambra. Kawun ta Cif Pius Ejimbe ne ya daga ta daga makarantar sakandare a Kano Nijeriya har sai da ta auri Marigayi Bennet Etiaba na Umudim Nnewi.[2]
Aiki
gyara sasheTa kwashe shekaru 35 tana aiki a matsayin malami sannan ta shugabanci makarantu da dama a Kafanchan, Aba, Port Harcourt, da Nnewi . Ta yi ritaya daga aikin Gwamnatin Jihar Anambra a 1991 kuma ta kafa Makarantun Tunawa da Bennet Etiaba, Nnewi, wanda ta kasance mallakin ta. A watan Maris na 2006 ta yi murabus domin karbar mukamin Mataimakin Gwamnan Jihar Anambra.
Etiaba ta kasance mamba a kungiyar mata ‘yan kasuwa, Shirin Ilimi na kasa da kasa na karamar hukumar Nnewi ta Arewa, da Environmental International Vanguard da kungiyar kula da ilimin yara ta duniya (OMEP). Ta kuma kasance membobin kungiyar Synod na Cocin na Najeriya (Anglican Communion), memba a kungiyar Kiristocin Makarantun Najeriya, memba a kwamitin gwamnoni na Makarantar Grammar Memorial ta Okongwu ta Nnewi, memba a kwamitin gwamnonin yara masu tsarki. Makarantar Convent, Amichi da kuma essoran sanda mai kula da Kotun Matasa na gundumar Nnewi.
Etiaba ita ce mahaifiyar yara shida wanda ɗayansu shine Emeka Etiaba (SAN), wanda ya taɓa tsayawa takarar kujerar gwamna a jihar Anambra.
Manazarta
gyara sashe- ↑ Azikiwe, Ifeoha (2013-04-17). NIGERIA: ECHOES OF A CENTURY: Volume Two 1999-2014. AuthorHouse. ISBN 978-1-4817-2929-1.
- ↑ https://books.google.com.ng/books?id=PDoIDEXdZwkC&pg=PA159&lpg=PA159&dq=Benjamin+Elue+2003+deputy&source=bl&ots=OBU2dqWtbH&sig=ACfU3U2w73O0Mhk6odVHLfhCY2nJ6lxzug&hl=en&sa=X&ved=2ahUKEwjt_r3wpurwAhVjhv0HHQbZCHEQ6AEwFXoECCUQAg#v=onepage&q=Benjamin%20Elue%202003%20deputy&f=false