Dambun nama
Dambu nama sanannen abun ciye-ciye ne na nama a Arewacin Najeriya kuma ana yawan shirya shi yayin bukukuwan Sallah na Musulmi. Zaɓin nama don yin wannan abun ciye-ciye na Sal-ah rago ne amma kuma ana amfani da naman sa da kaza.
Dambun Nama wani nau'in abincin kwadayine wanda hausawa ke sarrafa naman kamar Naman Kaji da naman Shanu da naman rago wajen komawa Kaman Dambu. Ana dafa naman ne sai a Daka shi har yayi sumul sannan sai a soya shi da mai.[1]
Yadda ake Dafa Dambun Nama
gyara sasheKi wanke nama sosai ki dora a wuta. Ki zuba kayan kamshi da albasa ki rufe ki barshi ya dahu sosai. Ki zuba maggi da salt. [2]