Dambun masara
Dambun masara wani nau'i ne na abincin hausawa, Wanda akeyinsa da barzajjen garin masara.
Ana yinsa ne da madambaci, ko buhu da wasu kanyi amfani dashi a yanzu. Shi dai Dambun masara akan cisa ne da man kuli-kuli, dukda wasu kan ci sa da man ja ko miya, ya danganta da yanda kake so.