Ciffati
Yana daya daga cikin abincin hausawa,yanda akeyin sa
Kayan haɗin da ake buƙata yayin haɗa ciffati shi ne:
1- Fulawa
2- siga
3- yis
4- gishiri
Da farko ki samu fulawa gwangwami biyu, ki samu sugar gwangwamin madara daya, ki jiqa shi daidai kar ki sa ruwa da yawa yadda za ki dama ba tare da ya yi ruwa da yawa ba, sai ki saka yis da gishiri kadan a cikin ruwan sugar.
Idan ya jiqa sai ki zuba akan fulawan, ki dama ya yi ruwa ba sosai ba amma, kamar cincin, sai ki ajiye a rana ki bar shi ya tashi, sai ki dinga diba kina soyawa kamar kurasa ko qwalan.
Za a iya ci da tea.