Bulo wani abu ne da ake amfani da shi wajan ginin kasuwanni, gidaje, makarantu, masallatai da sauran su. Ana haɗa bulo ne da kasa ko kuma kuma da siminti. Sannan na simintin ma akwai na kankare da kuma wanda siminti ne zalla.[1] An fara amfani da bulo na zamani ne tun akalla a 1930s, kafin nan ana amfani da itace ne da turbaya. A wancan lokacin ana hada bulo ne daga burbushin duwatsu da kuma ragowar kayayyakin masana'antu kamar breeze sai yasa akan kirasu da breeze block a tuance.[2]

hada bulo

Tarihi ya nuna cewa ana gine-gine na gidaje da katangu kamar irinsu Mashahurin Katangar Birnin Sin, sannan kuma masarautun Hausa ma zagaye suke da ganuwa, kamar Ganuwar Katsina, Zaria, Daura da makamantansu. Sai dai bayanai sun nuna cewa an fara amfani da bulo na zamani ne a shekarun 1930.[2]

Girman bulo na zamani ya kai kimanin tsayin 440 mm x 215 mm da kuma fadi nau'i daban daban daga 50mm zuwa 300mm.

Manazarta

gyara sashe