Bukka

Bukka wani ƙaramin ɗakin Fulani ne wanda sukeyi don ɗan wani lokaci

Bukka wani ɗan ɗaki ne (tanti) na wucin gadi wanda Fulani makiyaya ke amfani da shi lokacin da suka tashi don zuwa kiwon shanun su. Bukka tana karesu daga ruwan sama, sanyi da iska, haka suna tsara ɗakin yadda zaiyi kyau sosai. Galibi matan Fulani sune suke yin Bukka. Bukka tana samar da matsuguni ga fulani makiyaya, waɗanda ke kiwon garakunan shanun su a cikin dazuzzuka.[1][2][3][4][5][6]

Bukkar Fulani

Yadda akeyin Bukka

gyara sashe

Bukka ta kasu kashi biyu akwai bukkar da fulani sukeyi ta zama na din-din-din akwai kuma wadda suke yinta don zaman dan wani lokaci kamar wata daya zuwa biyu har fiye da hakan ma. Akwai bukkar da Fulani sukeyi kwana daya, biyu ko kwana uku har zuwa sati biyu dai, ita wannan bukkar sunayinta a matsayin ta wucin gadi, sunayin ta da kananun itace sai su haka rami kadan su kafa su sanya mata ganye kadan a ƙasa. Bayan sun gama kafa ginshiƙan bukkar sun haɗesu, sai su rufe saman bukkar da leda mai faɗi, saboda maganin ruwa ko kuma raɓa.

Manazarta

gyara sashe
  1. "Art and the Fulani/Fulbe People" (in Turanci). met museum.org. 2002. Retrieved 30 May 2024.
  2. "Housing And Furnishings". encyclopedia.com (in Turanci). Retrieved 8 June 2024.
  3. McKenna, Amy (17 May 2024). "Fulani people" (in Turanci). Britannica. Retrieved 19 June 2024.
  4. Hart, Benjamin L. "Applied ethology in a nomadic cattle culture". www researcgate.net. Retrieved 20 June 2024.
  5. Ford, Robert (27 May 2015). "Nomadic Fulani Hut dry season Sahel Burkina Faso West". iStockphoto.com. Retrieved 20 June 2024.
  6. "5 things you should know about Fulani tribe". pulse.ng. 12 February 2021. Retrieved 24 June 2024.