Bilk
Bilk wani yanki ne (Stadtteil ) a Düsseldorf. Tare da Oberbilk, Unterbilk, Hamm, Flehe da Volmerswerth sun ƙunshi gundumomi/yanki guda uku 3, wanda shine yanki mafi yawan jama'a na Düsseldorf. Bilk yana da girman 6.07 square kilometres (2.34 sq mi),[1] da 41,150 mazauna (2020).[2] Jami'ar Heinrich-Heine tana cikin garin Bilk.
Bilk | |||||
---|---|---|---|---|---|
locality of Düsseldorf (en) | |||||
Bayanai | |||||
Ƙasa | Jamus | ||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Jamus | ||||
Federated state of Germany (en) | North Rhine-Westphalia (en) | ||||
Government region of North Rhine-Westphalia (en) | Düsseldorf Government Region (en) | ||||
Urban municipality in Germany (en) | Düsseldorf | ||||
District of Düsseldorf (en) | District 3 (en) |
Tarihi
gyara sasheA farkon ambaton Bilk shine shekara ta 799. Tsohon Cocin ya tsufa kuma yana da alama ya kasance daga kusan 700 AD, wanda Saint Suitbert ya ba da shi, amma wuta ta lalata shi kusan 900, kuma an ambaci shi a cikin 1019 a karon farko. A cikin ƙarnuka masu zuwa, an sake gina cocin akai-akai, musamman a ƙarni na goma sha biyu 12 da na goma sha bakwai 17.
Har zuwa shekara ta 1206 yankin kamun kifi dusseldorp, wanda ke Arewacin Bilk, ya kasance na Ikklesiya Bilk. Bayan ranar sha hudu 14 ga watan Agusta na shekara ta 1288 ( Yakin Worringen ) Düsseldorf ya sami Haƙƙin Birni, Tsohon Bilk Church ya zama cocin birni. A cikin shekara ta 1380 gundumar /yanjun Berg ta zama Duchy na Berg, Düsseldorf babban birnin duchy. A cikin shekara ta 1384 ƙauyen Bilk (kudancin Tsohon Cocin Bilk, wanda mallakar Düsseldorf ne tun daga farko) ya zama wani yanki na birnin Düsseldorf.
Tun daga shekara ta 1852 a Kudancin Düsseldorf an sami bunƙasa masana'antu a lokacin juyin juya halin masana'antu . Düsseldorf ya girma zuwa kudu kuma cibiyoyin masana'antu na birni na al'ada suna nan har yanzu. A cikin shejarar ta 1893 Hammer Eisenbahnbrücke - gadar jirgin kasa a kan kogin Rhine - an gama. Bilk ta samu tashar jirgin kasa ta kanta, wacce a yau tashar jiragen kasa ce kawai ta yankin. An kafa Bilk Observatory a cikin shekara ta 1843 kuma an lalata shi ta hanyar bam a shekara ta 1943. A cikin shekara ta 1852 an sami asteroids 24 a wurin, wanda ake kira 24 Düsseldorf planets . An gina sabon tashar jiragen ruwa na Düsseldorf tsakanin sheakara ta 1890 zuwa shekara ta 1896, amma bayan da wata masana'anta ta karafa ta rufe aikinta, tashar ta rasa muhimmancinta. A cikin shekara ta 1990 an rufe babban sashi kuma an cika shi. Masana'antar watsa labarai ta zauna a wannan ƙasa kuma cibiyar al'adu ta girma. A cikin shekara ta 1999 gine-ginen Gehry sun kammala sabon taron.
Kayan aiki
gyara sasheTashar Düsseldorf-Bilk yanzu tana aiki ne kawai ta Rhine-Ruhr S-Bahn (jiragen jiragen ƙasa masu sannu a hankali) kuma ana haɗa su ta layin S 8, S 11 da S 28 zuwa Neuss, Mönchengladbach, Kaarst, Wuppertal, Hagen, Erkrath, Mettmann, Dormagen, Cologne da sauran sassan Düsseldorf ( Tashar Tsakiya, Düsseldorf-Gerresheim ,. . . ).
Layukan Tram suna haɗa Bilk tare da gundumar/yankin tsakiyar Düsseldorf da sauran gundumomi da yawa, musamman tare da kudancin birnin, Neuss, Ratingen, da jami'a. Haka kuma, layukan bas suna haɗa Bilk da sauran sassan birnin da garuruwan da ke makwabtaka da su.
Gine-gine da abubuwan jan hankali
gyara sashe- Alte Bilker Kirche (Tsohon Saint Martin Church), gini mafi tsufa a Düsseldorf
- Bilker Kirche (Cikin Saint Martin)
- Polizeipräsidium (1929-1932) da Oberfinanzdirektion (1929-1939)
- Rheinturm (mai tsayi 240.5 m)
- Düsseldorfer Stadttor (ya lashe wasu lambobin yabo na gine-gine)
- K21 - Kunstsammlung Nordrhein-Westfalen
- Lambun Botanic Düsseldorf
- Gine-ginen Gehry a cikin Harbour
Shahararrun mutanen da suka zauna a Bilk
gyara sashe- Johann Friedrich Benzenberg an haifeshi a shekara ta (1777-1846), masanin ilmin taurari
- Ferdinand Freiligrath (1810-1876)
- Maria Melos an haifeshi a shekara ta (1820-1888)
- Ferdinand Lassalle an haifeshi a shekara ta (1825-1864), daya daga cikin wadanda suka kafa Jam'iyyar Social Democratic Party ta Jamus.
- Heinrich Spoerl an haifeshi a shekara ta (1887-1955), marubuci kuma ɗansa Alexander Spoerl an haifeshi a shekara ta (1917-1978), marubuci.
- Jakob Salentin von Zuccalmaglio an haifeshi a shekara ta (1775-1838), masanin shari'a
- Heino an haifeshi a shekara ta (1938)
Adabi
gyara sashe- Udo Achten (Hrsg. ): Düsseldorf zu Fuß, 17 Stadtteilrundgänge durch die Geschichte und Gegenwart . 1. Aufl., VSA-Verlag, Hamburg 1989
- Karl Endmann: Düsseldorf und seine Eisenbahnen a cikin Vergangenheit da Gegenwart . 2. Aufl., Motorbuch Verlag, Stuttgart 1987
- Oswald Gerhard da Wilhelm Kleeblatt (Hrsg. Düsseldorfer Sagen aus Stadt und Land . Werkgetreue Neuausgabe von 1926, Verlag der Goethe-Buchhandlung, Düsseldorf 1982
- Karl Emerich Krämer: Durchs Düsseltal nach Düsseldorf . 1. Aufl., Mercator-Verlag Gert Wohlfahrt, Duisburg/München 1968
- Sonja Schürmann: Düsseldorf, Eine moderne Landeshauptstadt mit 700jähriger Geschichte und Kultur . 1. Aufl., DuMont Kunst-Reiseführer, Köln 1988
- Hermann Smeets: Villa Bilici. Düsseldorf-Bilk früher und heute . 1. Aufl., Herausgegeben von der Stadt-Sparkasse Düsseldorf, Triltsch Druck und Verlag, Düsseldorf 1983
- Hugo Weidenhaupt: Kleine Geschichte der Stadt Düsseldorf . 4. Aufl., Verlag L. Schwann, Düsseldorf 1968
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Stadtgebietsprofile - Stadtbezirke und Stadtteile 03 Geografie" (PDF). Landeshauptstadt Düsseldorf. Retrieved 4 November 2022.
- ↑ "Stadtgebietsprofile - Stadtbezirke und Stadtteile 05 Bevölkerung" (PDF). Landeshauptstadt Düsseldorf. Retrieved 4 November 2022.
Hanyoyin haɗi na waje
gyara sashe- Go-Bilk (in German)
- Yanar Gizo daga Bilk a Duesselgo.de Archived 2023-05-25 at the Wayback Machine (in German)
- Bilker Heimatfreunde (in German)
- Stadtteilinfos (in German)
- Katholische Pfarrgemeinde St. Martin Bilk-Friedrichstadt Archived 2005-09-12 at the Wayback Machine (in German)
- Evangelische Friedens-Kirchengemeinde Bilk-Unterbilk-Friedrichstadt (in German)
- K21 tarin fasaha