Biambasuren Luvsandamdingiin (an haife ta a shekara ta 1955) ita masaniyar gine-ginen Mongolian ce.

Biambasuren Luvsandamdingiin
Rayuwa
Haihuwa 1955 (68/69 shekaru)
ƙasa Mangolia
Karatu
Harsuna Mongolian (en) Fassara
Sana'a
Sana'a Masanin gine-gine da zane da urban planner (en) Fassara

Ta yi karatunta na gine-gine a Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Mongolian, ta kammala a cikin shekara 1978. An nada mata suna mai zane-zane na Cibiyar Zane-zane ta Jiha. A matsayinta na mai tsara birane, ta yi manyan tsare-tsare na birane da garuruwa a cikin Mongoliya. A shekara ta 1983, ta ɓullo da wani shiri na birnin Khovd wadda ta adana tsofaffin sassan birnin tare da sake gina sabbin sassan birnin. Shirin nata ta sami lambar yabo ta Laureate daga Ƙungiyar Ƙwararru na Mongolian. Tun daga shekara 2007, tana aiki da birnin Khovd a matsayinta na mai tsara birane.