Bayanau

kalmar da take kara bayani akan wani aiki

Bayanau kalmomi ne da ke yin ƙarin bayani game da aikatau. Wannan bayani da suke yi shi ya ke fito da aikin a fili. Sukan faɗi gurin da aka yi aikin, lokacin da aka yi aiki ko kuma yadda aka yi, ake yi ko za a yi aiki.

bayanau
bangaren magana
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na content word (en) Fassara
Gajeren suna ADV
Described at URL (en) Fassara glottopedia.org…, glottopedia.org…, glottopedia.org… da lexicon.hum.uu.nl…
Represents (en) Fassara condition (en) Fassara
Amfani wajen Universal Dependencies (mul) Fassara
Entry in abbreviations table (en) Fassara م ف, zf., ق da bw.
bayanau
bangaren magana
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na content word (en) Fassara
Gajeren suna ADV
Described at URL (en) Fassara glottopedia.org…, glottopedia.org…, glottopedia.org… da lexicon.hum.uu.nl…
Represents (en) Fassara condition (en) Fassara
Amfani wajen Universal Dependencies (mul) Fassara
Entry in abbreviations table (en) Fassara م ف, zf., ق da bw.
Bayanau
Bayanau

Ma’anar Bayanau

gyara sashe

Masana suka ce, kalma ce da ke yin ƙarin bayani game da aikatau a cikin jimla. Wato kenan, wannan kalma, ita ce fitilar da take haskaka aikatau a ganshi a fahimce shi.

Rabe-Raben Bayanau

gyara sashe
  • Bayanau na wuri.
  • Bayanau na lokaci.
  • Bayanau na yanayi.
  • Bayanau na Wuri

Bayanau, kalmomi ne da ke yin bayanani game da aikatau a cikin jimla. Bayanau ya rarrabu zuwa bayanau na wuri wanda ke bayyana wurin da aka yi aiki, ko za a yi ko kuma ake cikin yin aikin. Sai kuma bayanau na lokaci, wanda ke bayyana lokacin da aka yi aikin, ko za a yi ko kuma ake cikin yin aiki. Haka nan kuma akwai bayanau na yanayi, wanda shi kuma nuni yake zuwa ga yadda aka aiwatar da aikin, ko za a aiwatar ko kuma ake aiwatar da aikin. [1]

Manazarta

gyara sashe

[2]

  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2019-08-11. Retrieved 2021-03-11.
  2. Bunza A.M. (2002). Rubutun Hausa Yadda Yake da Yadda Ake Yin Sa Don Masu Koyo da Koyarwa. Irshad Islamic Publication Cetre LTD. 31, Adelabu Street, Surulere, Lagos-Najeriya. Jinju M.H. (1981). Rayayyen Nahawun Hausa. Northern Nigerian Publishing Company Limited. Sani M.A.Z. (1999). Tsarin Sauti da Nahawun Hausa. University Press PLC, Ibadan - Najeriya. Sani M.A.Z., Muhammad A., da Rabeh B. (2000). Exam Focus Hausa Language Don Masu Rubuta Jarabawar WASSCE da SSCE. University Press PLC, Ibadan - Najeriya. Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 1. University Press PLC, Ibadan-Nigeria. Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 3. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.