Batiar
Batiar (ana kuma rubuta shi a matsayin baciar), sanannen suna ne na wasu nau'in mazauna birnin Lviv. Ana ldaukarta a matsayin wani ɓangare na ƙananan al'adun birnin, salon rayuwar "knajpa" na Lviv, kuma ya zama sabon abu a farkon karni na ashirin duk da cewa tushensa ya samo asali ne daga tsakiyar karni na sha tara. Ya ja baya baya da Tarayyar Soviet ta mamaye Gabashin Poland da kuma mamaye ta zuwa Tarayyar Soviet a matsayin wani ɓangare na SSR na Ukrainian a shekarar 1939 da kuma a 1945. Hukumomin Tarayyar Soviet sun kori yawancin mazauna Poland kuma sun watsa al'adun Poland. Duk da haka, an cigaba da amfani da kalmar, kuma sanannen kalmace na ƙauna a Lviv a yau. Tun daga shekara ta 2008 Lviv ta cigaba da bikin "Ranar Baitat na Kasa da Kasa wato International Batiar Day", wanda kamfanin "Dik-Art" ta fara tare da hadin gwiwa da Majalisar Birnin Lviv. [2]
Batiar | |
---|---|
subculture (en) | |
Bayanai | |
Ƙasa | Ukraniya |
Wuri | |
Ƴantacciyar ƙasa | Ukraniya |
Oblast of Ukraine (en) | Lviv Oblast (en) |
Raion of Ukraine (en) | Lviv Raion (en) |
Hromada (en) | Lviv urban hromada (en) |
City in Ukraine (en) | Lviv (en) |
Batiary, to dzieci so lwoskij ulicy
Wysoły, z fasonym, skory du kantania:
Na takich gdzi indzij mówiu "ulicznicy"
z tomiku" Krajubrazy syrdeczny".[1]
Tushen kalmar
gyara sasheAsalin kalmar na iya fitowa daga harshen Hungary, tunda a cikin karni na 19 Lviv wani yanki ne na daular Austro-Hungary, wasu daga cikin 'yan sandanta sun kasance 'yan kasar Hungary ne kuma sun kawo kalmar zuwa yaren gida daga yarensu na asali.
Ma'anar kalmar acikin Encyclopædia Britannica :
Betyar (pl. betyarok) a highwayman in 19th-century Hungary. The word is Iranian in origin and entered the Hungarian language via Turkish and Serbo-Croatian; its original meaning was “young bachelor” or “lad.” While most betyárok were originally shepherds, whose position in rural society was marginal, many were army deserters or young men fleeing conscription. They are first mentioned in legal documents about 1800.
Tarihi
gyara sasheSunan ƙananan mazaunan Lwów ne ("attajiran Lviv"). Batiars suna magana na musamman da harshen Poland, wanda ake kira Bałak kuma yana da bambanci da yaren Lwów. Batiar na yau da kullun a cikin tunanin kowa sun kasance talakawa ne, amma sun kasance wayayyu masu gaskiya da karimci tare da nishadantarwa. Daga cikin mashahuran batiar, akwai irin waɗannan sunaye kamar ma'aikatan gidan rediyo Kazimierz Wajda da Henryk Vogelfänger na gidan rediyon Wesoła Lwowska Fala wanda yayi fice, da kuma tauraron ƙwallon ƙafa Michał Matyas, wanda ya buga wa Pogoń Lwów da tawagar ƙasar Poland.
Har yanzu ana amfani sunan a kauyuka, amma yanzu a cikin yaren Ukrainian . Yanzu batiars su ne playboys na Ukrainian Piedmont.
Sources
gyara sashe- Witold Szolginia, Batiar and his balak (in Polish)
- Homo leopolensis essay from under the "microscope of pan Yurko" (in Ukrainian)
- Definition of Betyar by Encyclopædia Britannica (in English)
- The Batiar's Day report by "UkrInform" (in Ukrainian)
- Phenomenon of Lwow's "knajpa" (in Polish)
- Biesiady i Combry from Agencja Artystyczna (Ta-joj, Europo! - Biesiada Lwowska) (in Polish)
- Batiar's of the Ukrainian Lviv Archived 2008-07-25 at the Wayback Machine (in Ukrainian)
Manazarta
gyara sashe- ↑ Batiar i Jego Balak (in Polish)
- ↑ "Dik-Art" website