Banku da Tilapia abinci ne na gargajiya daga Ghana, kuma ana matukar son sa musamman a kudancin kasar.[1] Banku wani nau'in abinci ne da ake yi da masara da ciyawa ko kuma shinkafa. Ana daka masarar sannan a gauraya ta da ruwa a bar ta ta kwana domin ta tsufa ko ta tsuma, bayan haka sai a dafa ta cikin tukunya har sai ta yi kauri sosai kuma ta zama tauri.[2] Tilapia kuwa kifi ne da aka soya ko aka gasa tare da kayan kamshi irin su tafarnuwa, albasa, tumatir, da barkono. Ana ci banku tare da tilapia, kuma ana iya ci da miya mai daddawa wadda aka hada da kayan lambu ko barkono mai zafi.[3]

Banku da Tilafiya
Banku da tilafiya

Yadda ake dafa Banku

gyara sashe
  1. Garin Masara A niƙa masara da kyau har sai ta zama gari mai kyau.
  2. A hada garin masarar da ruwa sannan a barshi ya juƙu na tsawon kwanaki 1 zuwa 2 don ya yi fermenting.
  3. Dafa GarinA sa a tukunya sannan a dafa shi da ruwa me zafi mai tsanani har sai ya yi kauri.
  4. Suya ko Gasawa A soya ko a gasa kifin Tilapia tare da kayan kamshi kamar tafarnuwa, albasa, da tumatir da citta da barkono.

Mahimmancin Banku da Tilafiya

gyara sashe

Banku da Tilapia abinci ne mai matukar muhimmanci a al’adun Ghana. [4] Yana da alaka da taron dangi da al’adun yammacin Afirka, kuma ana ci musamman a lokutan bukukuwa ko lokutan hutu tare da iyali da abokai.Banku na dauke da sinadarin carbohydrate daga masara wanda ke samar da kuzari, yayin da kifin tilapia yake samar da protein wanda ke da matukar muhimmanci ga lafiyar jiki.

Manazarta

gyara sashe
  1. name=https://cultureandspices.com/banku-and-tilapia/
  2. name=https://www.bigstarafrocuisine.com/product/banku-with-grilled-tilapia/
  3. name=https://www.maggi.ng/recipes/tilapia-quick-traditional
  4. name=https://firstpalacerestaurant.com/product/banku-tilapia/[permanent dead link]