Balangu
Naman Balangu
gyara sasheNaman Balangu wani nau'in nama da ake yi akasar hausa, sigar gargajiya ce da ake hada nama akan wuta tare da hada masa kayan ɗanɗano masu dadi da kanshi.
Salo wadda ta samo asali daga ƙasar Hausa, Arewacin Najeriya, kuma abinci ne da ya shahara a yammacin Afirka. Balangu wani yanki ne mai girma na al’adun Hausawa da abinci, kuma mazajen Hausawa ne ake shirya su kuma suke yin su, don haka ake kira ‘Mai nama’ (ba mata ba).[1] Ana yin Suya ne da naman sa, rago, tukunkiya, sa ko kuma akuya, amman mafi yawanci anfi amfani da kananun dabbobi kamar rago da tunkiya.