Azumi Namadi Bebeji
Azumi Namadi Bebeji (an haife ta ranar 5 ga watan Yuni, 1950) a wani kauye da ake kira da Bebeji, wani tsohon gari ne da ke Kano, a tarayyar Najeriya. [1]
Kuruciya da Ilimi
gyara sasheAn haife ta a ranar 5 ga watan Yuni shekara ta alif ɗari tara da hamsin 1950, kuma ta fara karatu a lokacin tana da shekaru 7 a makarantar St. Theresa (Makarantar Catholica, Jos) inda ta kammala Karatun ta na firamare. Daga shekara ta alif ɗari tara da tamanin da daya 1981 zuwa 1988 ta cigaba da karatun ta a makarantar Women Teachers College (WTC), Gidan Galadima, Kano sannan ta cigaba da karatun koyarwa (GCE) a shekarar 1986. Bayan ta samu shaidar karatun koyarwa na biyu (Grade II) a WTC, hakan ya bata daman shiga Jami’ar Abuja a shekara ta 2003, inda tayi karatu a fannin siyasa (Political Science).[2]
Siyasa
gyara sasheA shekara ta 1999, ta fito takarar kujerar Majalisar dokoki mai wakiltar mazabar Kiru/Bebeji a karkashin jam’iyyar PDP, kuma tayi nasarar lashe zaben.
Rayuwar iyali
gyara sasheAzumi Bebeji ta kasance mabiyar addinin musulunci, tayi aure kuma ta’ haifi yara.