Rayuwar sa gyara sashe

An haifi farfesa Auwalu Uba ne a shekarar 1964 miladiya 18 ga watan Fabrairu, a garin Hardawa wanda yakƙ garamar hukumar Misau na Jihar Bauchi ƙ gasaN najeriya. Wanda yanzu yana zaune ne ƙ gasar ta Najeriya a garin na Bauchƙ garamar Hukumar Misau.

Karatun sa gyara sashe

Ya fara karatu a Makarantar Central primary school Hardawa a shekarar 1972 zuwa 1978 sannan ya tafi zuwa Government School Misau daga shekarar 1978 zuwa 1982, Daga nan ne yasamu takardar chanjin makaranta zuwa Government Science Secondary School Azare a shekarar 1982 kuma a nanne ya kammala karatun sakandari a shekarar 1983.

Farfesa yayi makarantar Basic Studies (SBS) Ta Zaria daga shekarar 1983 zuwa 1984; Sa'annan yasamu Damar shiga Makarantar ta Ahmadu Bello University Zaria, A bangaren kimiyya na Karatun ƙananun Halittu (Microbiology). Kuma ya kammala digirin sane a shekarar 1987.[1]

Yayi Bautan ƙasar sane a General Hospital Katsina, na Garin Kastina a Najeriya, yayi Digiri na biyu (Masters) a University na Maiduguri a shekarar 1992, Sannan kuma yayi PHD a Medical Microbiology a shekarar 2004 a Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa.

Ya cigaba da ziyartar wadansu manazarta a Jami'ar Wales, Swansea a Engila daga shekarar 2000 zuwa 2001, Ya fara matakinsa na matsayin Graduate Assistants a shekarar 1989 tare da jami'ar Maiduguri, A watan Yuli na shekarar 1995 ya fara aiki a Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa Bauchi a matsayin Lakchara 2,

Ya zama lakchara 1 a shekarar1998 sannan kuma ya zama Associate Farfesa a shekarar 2004 sannan kuma ya zama Farfesa a shekarar 2007.

Sanan daga nan ne ya samu damar zama Vice chancellor a Jami'ar Jihar Bauchi mai suna BASUG.

Kuma mamba ne a American Society of Microbiology, Applied Microbiology na United Kingdom da kuma Nigerian society of Microbiology.

[1]

Aikin sa gyara sashe

Farfesa Ma'aikacin gwamnatine a fannin koyarwa wanda yakai matakin farfesa a bangaren (Microbiology)

Kuma ya riƙe mastayi daban daban a gwamnati[2]

Matakan da ya riƙe A Jami'a gyara sashe

  1. Mai Kula da Jarabawa (Exams Officer)
  2. Mamba (Departmental post graduate committee)
  3. Mamba (Student welfare Board A.T.B.U)
  4. Mamba (University Senate A.T.B.U)
  5. Mamba (Senate exams misconduct committee A.T.B.U)
  6. Shugaban kula da Dalibai (Dean Student Affairs)
  7. Shugaban Dept (HOD Biological science)
  8. Darecta a (Endowment) A.T.B.U
  9. VICE CHANCELLOR BASUG


Manazarta gyara sashe

  1. 1.0 1.1 ="https://arewaaffairs.blogspot.com/2017/12/profile-of-new-vc-of-basug-prof-auwal.html?m=1">https://arewaaffairs.blogspot.com/2017/12/profile-of-new-vc-of-basug-prof-auwal.html?m=1 Cite error: Invalid <ref> tag; name ":0" defined multiple times with different content
  2. https://africaprimenews.com/2021/11/prof-auwal-uba-bags-award-for-excellence-as-bauchi-state-univ-emerges-centre-of-excellence/?amp=1