Aure a Ƙasar Hausa Aure wata l alaƙa ce ta halascin zaman tare a tsakanin namiji da mace. Ana yin aure domin abubuwa da dama, daga ciki akwai kariya daga zina, samun nutsuwa da kwanciyar hankali, samawa abin haihuwa, dama sauran abubuwa,

Haka ake taruwa yayi daura auren hausawa
yanda hausa ke taruwa Wajen daurin aure
ango

Akan samu bambance-bambancen al’adu daga yanki zuwa wani yankin a ƙasar Hausa. Amma akwai gama-garin abubuwa, waɗanda ko’ina ana yinsu kamar taron Jama'a, taya murna da dai sauransu

Da

Neman Aure

gyara sashe

Hanya ta farko ita ce saurayi ya ga budurwa yana so. Idan haka ta faru to ba shi zai yi mata magana kai-tsaye da kansa ba, zai samu babban abokinsa wanda suka amince wa juna ya sanar da shi, idan shawararsu shi da abokin nasa ta yi daidai, to shi abokin nasa ne zai yi wa budurwar magana. Ko kuma wani daga cikinsu (saurayin ko abokin nasa), ya samu kawar budurwar ya gaya mata ita kuma ta isar da sakon zuwa ga wacce ake so. Idan aka samu dacewa a tsakaninsu, to shi ke nan.

  • Hanya ta biyu kuma ita ce ta hanyar kamu: Kamu a neman aure shi ne idan iyayen yaro suka ga wata yarinyar da aka san gidansu mutanen kirki ne, sai su ce muna kamu ko mun yi wa wane kamu. Ta irin wannan sigar ce ake samun abokai maza ko kawaye mata su hada ’ya’yansu aure.

kyauta Kyauta ita ce mataki na biyu a cikin neman aure. Ita wannan kyauta shi mai nema ko iyayensa ne ke kai kyautar gidan matar da za a nema. Daga nan kuma sai iyayen yarinya su ba da dama shi mai nema ya fara zuwa ko dai kai-tsaye gidan matar da za a nema ko kuma gidan wadansu makusantan iyayen nata wadanda ake kyautatawa zaton ba za su bari wani abu na lalata ya shiga tsakanin saurayin da budurwar ba.[1] lefe Lefe shi ne mataki na uku na neman aure. Lefe kayayyaki ne da ake hadawa da suka shafi tufafi da kayan kwalliya gwargwadon karfin mai nema, a zuba su cikin lefe, daga baya ya koma fantimoti, ko kwalla ko akwatu. A wannan zamanin na yanzu kuma akwatu mai taya, a kai gidan su yarinyar da ake nema. Yawanci mata daga bangaren mai nema su suke kai wadannan kayayyaki. Baiko Baiko shi ne tabbatarwa da wanda za a baiwa yarinya da aure cewa an bashi. Akan raba ɗan abin masarufi kamar irin su alewa da sauran su ga jama’a; musamman makusantan saurayin da budurwar, domin su sheda cewa an tsayar wa da yarinya mijin aure.[2]

saka ranar biki Tsayar da rana ko saka rana, al’ada ce da ake daukar wasu kayayyaki daga gidan mai neman aure, zuwa gidan wacce ake son aura, daga nan sai dukan bangarori biyu su tsayar da wani lokaci mai zuwa a matsayin ranar da za a hadu a daura aure. Daga cikin irin kayayyakin da ake kaiwa akwai goro, alawa (minti), tabarma, kudi da sauransu wadanda kan bambanta daga guri zuwa guri.

Daurin aure

gyara sashe

Ana ɗaura aure a Ƙasar Hausa ta hanyar tara jama’a a ƙofar gidan mahaifin yarinya ko kuma waliyinta. Kayayyakin da ake tanada sun haɗa da:

Sadaki, kuɗi ne waɗanda iyayen yarinya ke ayyanawa a bisa ƙa’idar aure (Habib, Usman, da Rabi’u, 1982).

Waliyayyai: Mutane ne guda biyu da ɗaya ke tsayuwa ta ɓangaren yarinya (walin ‘ya mace) da kuma ɗaya da ke tsayuwa ta ɓangaren ango (walin ɗa namiji), waɗanda ke a matsayin wakilan ango da na amarya. Shaidu, su ne jama’ar da ake tarawa waɗanda ke taruwa don su zama shedar cewa daga wannan rana wance ta zama matar wane. Goro da kuɗin ɗaurin aure: Shi goro ana rarraba wa dukkan jama’ar da suka taru a wannan waje ne. Su kuma kuɗin akan bawa walin ‘ya mace, malamai masu addu’a, da kuma abokan wasanta maza (kuɗin mijin baya).

Adduar daurin Aure

gyara sashe

Bayan jama’a sun taru, gidajen biyu sukan koma gefe su zauna, sai gidan maza (masu nema) su ce, “Mun ga abin da muke so gare ku”. Su kuma sai su mayar musu da tambaya su ce, “Mai kama da me?” Sai gidan miji su sake cewa, “Mata”. Daga nan sai su ɗan yi shiru wai sun yi shawara kenan, sai kuma babbansu ya amsa da cewa, “Mun baku bisa sunna”. Su kuma su ce, “Mun karɓa bisa sunna”. Idan aka gama wannan kuma sai a rarraba goron nan da aka zo da shi. Sannan kuma sai a koma ɓangaren liman shi kuma ya yi huɗubar ɗaurin aure sannan ya ce na ɗaura auren wance da wane bisa sadaki kaza, naƙadan ba ajalan ba. Idan kuma ajali ne sai ya ce, ajalan ba naƙadan ba. Sannan ya ci gaba da cewa, “Ciyarwa, shayarwa, tufatarwa, muhalli da koya addini suna kan wane ɗan wane, jama’a kun shaida?” Sai a amsa masa da cewa, “I, mun sheda”. Za a maimaita wannan har sau uku. Daga nan kuma sai liman ya yi addu’a sannan sai a sallami kowa ya kama gabansa.[3]

Yinin Biki

gyara sashe

Akasari ranar daurin aure ne ake yin yinin biki a gidan su amarya yan uwa da abokan arziki zasu taru a gidan wasu su kawo kudi ko kuloli, kofuna da dai sauran su suba uwar amarya zaa yi abinci kala kala yanda zaa ci a koshi

Kai Amarya a gidan Miji

gyara sashe

Bisa ga Aladar Bahaushe idan dare yayi sai abokan ango suzo da motoci da abokan amarya da iyaye a shiga a yi ma Amarya rakiya zuwa gidan mijinta in an kaisu kuma sai a dawo da su har gida amma zaa bar amarya a cen

walima itace bayan an kai amarya a gidan mijin ta to wan shekare yan uwa da abokan arziki zasu je gidan amaryar a taru wasu lokacin suke jera mata kayan daki lokacin zaa kai garan amarya sannan in duhu ya fara sai kowa ya tafi gida amma banda abokan amarya

Sayen Baki

gyara sashe

ranar walimar in kowa ya tafi gida sai abokan ango su taho da ango sannan amarya baza tayi magana ba sai an sayi bakin ta wato sai a ba abokan amarya kudi sannan ta bude baki tayi magana sannan abokan ango da abokan amarya kowa zai tafi su bar amarya da ango su kadai

Manazarta

gyara sashe
  1. https://aminiya.ng/aure-a-kasar-hausa/
  2. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-01-24. Retrieved 2024-03-12.
  3. https://aminiya.ng/aure-a-kasar-hausa/