Asusun Raya Mata na Afirka (AWDF), shi ne gidauniya ta farko da ke tallafawa ayyukan ƙungiyoyin kare Haƙƙin mata a yankin nahiyar Afirka. Bisi Adeleye-Fayemi, Joana Foster da Hilda M. Tardia ne suka kafa AWDF a cikin 2001. AWDF na cikin Ƙungiyar Ƙungiyoyin Mata ta Duniya, wata ƙungiya ta gidauniyar mata da ke mai da hankali kan tallafawa 'yancin ɗan adam na mata.

theo saw a rana magna kan cigaban Matan arewa a landan
musinbi rana magna akan kudon ci gaban mata a 2014

Nasarorin da aka samu

gyara sashe

Ellen Johnson Sirleaf, shugabar ƙasar Laberiya kuma wadda ta lashe lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel a shekara ta 2011, ta gabatar da lacca na cika shekaru goma na AWDF a wajen bikin da aka yi a birnin Accra na kasar Ghana a watan Nuwamba na shekarar 2010. shekara ta goma kun yi nasara a cikin manufofinku;

Tsakanin 2001 zuwa 2016 AWDF ta raba dalar Amurka miliyan 26 ga ƙungiyoyin kare Haƙƙin mata.

AWDF ta rattaba hannu kan wata takardar aiki don jagorantar nazari da ayyukanta a lokacin taron mata na Afirka da ya gudana a Accra daga 15 zuwa 19 ga Nuwamba 2016.

Bayanan da aka ambata

gyara sashe