Annabi Adam :shi ne mutum na farko wanda Allah ya halicce sa ba tare da mahaifa ba. Allah ya halicce sa ne daga kasa mai mabanbantan launika daban-daban, shi ne mutum da ya zamo uba ga dukkan wani mutum da Allah ya halitta a doran duniya na da da na yanzu da ma wanda zai zo nan gaba.