Anita Mugeni (an haife ta a shekarar 1970) alkaliya ce 'yar kasar Rwanda kuma shugabar kotun shari'a ta gabashin Afirka (EACJ) wacce ta kasance shugabar riko ta kungiyar lauyoyin kasar Rwanda. [1] [2]

Anita Mugeni
Rayuwa
Haihuwa 1970 (53/54 shekaru)
Sana'a
Sana'a mai shari'a da Lauya

Ilimi da aiki

gyara sashe

Anita Mugeni ta sami digirinta na farko a fannin shari'a daga Jami'ar Kasa ta Rwanda a shekarar 1996 sannan ta yi digiri na biyu a fannin shari'a daga FUSL-UC Louvain, Belgium a shekarar 2005. Ta fara aikin shari'a a 1998 a matsayin lauya. Ita ce abokiyar kafa ta MRB Attorneys. Ta kasance mamba a Majalisar Dokokin Gabashin Afirka, kuma ta yi aiki a matsayin kwamishiniyar Hukumar Kula da Ayyukan Jama'a da Kwamitin Ba da Shawarwari na Kasa kan Tarayyar Siyasa ta EAC. [1] An nada ta a Kotun daukaka kara ta Gabashin Afirka a shekarar 2021 hakazalika an nada ta a matsayin shugabar kotun a watan Mayun 2023 inda ta maye gurbin alkalin kotun Tanzaniya, Sauda Mjasiri bayan ta yi ritaya daga kotun. [3] [4] [5]

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 Karuhanga, James (2023-05-31). "Rwanda's Justice Anita Mugeni designated as EACJ Vice President". The New Times (in Turanci). Retrieved 2023-12-08. Cite error: Invalid <ref> tag; name ":0" defined multiple times with different content
  2. "8 judges appointed at East African Court". Monitor (in Turanci). 2021-03-04. Retrieved 2023-12-08.
  3. "Defender Profile: Rwandan Lawyer Anita Mugeni - International Bridges to Justice". www.ibj.org (in Turanci). 2009-07-15. Retrieved 2023-12-08.
  4. "Hon. Lady Justice Anita Mugeni – East Africa International Arbitration Conference 2023" (in Turanci). Retrieved 2023-12-08.
  5. "MSN". www.msn.com. Retrieved 2023-12-08.