Amos Tutuola
Amos Tutuola yayi rayuwa daga ashirin ga watan Yuni ta shekarar alif dari tara da ashirin zuwa takwas ga watan Yuni na shekarar alif dari tara da casa'in da bakwai. Shi marubuci ne dan kasar na Najeriya ya rubuta littattafai akan almara ta yarbanci.
Tarihin Rayuwa
gyara sasheAmos Olatubosun Tutuola Odegbami an haife shi a ashirin ga watan Yuni ta shekarar alif dari tara da ashirin a Wasinmi, kauye ne mil kadan daga wajen Abekuta a Najeriya, inda iyayenshi, Charles Tutuola Odegbami da Esther Aina Odegbami, wadanda yarbawa ne mabiya addinin kirista kuma manoman Koko suka yi rayuwa.
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.