Amina Namadi Sambo
Amina Namadi Sambo An haife ta a Jihar Kano, daga Ahalin Mallam Abdullahi Abubakar Lukat da kuma Hajiya Huwaila Abdu Abubakar Lukat. Ita ce ta uku a cikin yan'uwanta su goma sha daya.[1]
Amina Namadi Sambo | |
---|---|
Rayuwa | |
Sana'a |
Karatu
gyara sasheTa yi firamare dinta a makarantar Boro Boarding Primary dake Zaria sannan ta yi da dinta a Louis Secondary School Kano a cikin garin kano. Ta samu shiga Jami’ar Bayero ta Kano inda ta karanci harkokin siyasa kuma ta Gama a shekara ta 1989. Amina ta yi karatun Diploma a Arabic da kuma Islamic a Al-Manar International College Kaduna.[1]
Rayuwa
gyara sasheAmina Namadi Sambo mata ce ga tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Namadi Sambo. Lokacin mulkin su ta taimaka wa mata da yara. Ita ce shugabar ‘Nalado Nigerian Limited’, darakta ce a COPLAN Ltd.Ta baiwa mata tallafin magani kyauta. Ta ɗauki nauyin yi wa mutane ɗari da hamsin (150) ayyuka kyauta. Suna da yara shida (6) da mijinta, uku (3) maza, uku (3) mata.[1]
Bibiliyo
gyara sashe- Kabir, Hajara Muhammad,. Northern women development. [Nigeria]. ISBN 978-978-906-469-4. OCLC 890820657.
- Furniss, Graham. (1996). Poetry, prose and popular culture in Hausa. International African Institute. Edinburgh: Edinburgh University Press for the International African Institute. ISBN 978-1-4744-6829-9. OCLC 648578425.