Amfanin kabewa a jikin Dan Adam
Gabatarwa
gyara sasheHanyoyi da ake amfani da kabewa ga rayuwar al’umma suna da yawan gaske musamman ma ga lafiyar jiki, domin Hausawa na cewa “abincinka maganinka”. To ita kabewa Allah ya yi mata baiwa da yawa da take taimakawa, a jiki dan’adam ya samu ingantacciyar lafiya. Kuma ga ita kabewar ba ta da wuyar samuwa haka ma wajen sarrafata babu wata wuya. Ana miya da ganyen ko ‘ya’yan kabewan. Ga dai wasu daga cikin amfaninta.[1]
Gyaran Fata
gyara sashetana kare fata daga zafin ranar da ke wa fatar jikin mutum illa ya sa ta yi sumul-sumul. Da haka ne masana kiwon lafiya ke mata kirari da ‘mai maida tsohuwa yarinya’.[2]
Tana taimaka wa masu ciwon cutar sikari
gyara sashedomin tana rage yawan ‘Glucose’ bayannan kuma ta kara masu yawan ‘Insulin’ da jiki ke samarwa.
Tana riga-kafin cutar daji
gyara sasheKamar yadda cibiyar bincike a kan cutar daji ta kasar Amurka ta tabbatar da cewar, duk abincin da ya kunshi sinadarin da ake kira ‘betacarotene’ ya na ba jiki kariya daga cutar daji, kuma an tabbatar da cewar kabewa na dauke da wannan sinadarin mai yawa.
Lafiyar zuciya
gyara sashea cikin kabewa akwai wasu sinadarai
dake rage yawan ‘closteral’ a jikin dan’adam wanda hakan ke taimaka wa zuciya. Amma wannan ya na kunshe ne a cikin su ‘ya’yan kabewa.
Karin sha’awar jima’i
gyara sasheƳa’yan kabewa na Kunshe da wani sinadari da ake kira da suna ‘zinc’ wanda masana suka bayyana da cewar ¼ na cikin coffin na kunshe da kasha 17 na abin da mutum ke bukata na wannan sinadari a kullun wanda hakan ke kara sha’awa ga namiji.
Maganin gajiya
gyara sasheAkwai sinadarin ‘potassium’ wanda ya ke taimakawa wajen wartsakar da gajiya da ake fuskanta wajen aikace-aikacen yau da kullun. Ita kabewa na kunshe da wannan sinadarin.[3]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-03-28. Retrieved 2023-03-28.
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-03-28. Retrieved 2023-03-28.
- ↑ https://www.alummarhausa.com.ng/2020/10/amfanin-tumatur-da-kabewa-ga-lafiyar-jikin-dan-adam.html