Ambaliyar Ruwa ta Bukavu ta 2022
A farkon shekarar 2022, an yi ruwan sama kamar da bakin ƙwarya wanda ya haifar da ambaliya mai yawa a birnin Bukavu da ke kudancin Kivu a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.[1]
Iri | aukuwa |
---|---|
Abubuwan da suka faru
gyara sasheA ranar 22 ga watan Fabrairu, 2022, mutane shida ciki har da yara huɗu sun mutu bayan ruwan sama mai ƙarfi ya haddasa ambaliya.[2]
A ranar 16 ga watan Maris, ambaliyar ruwa ta afku a birnin Bukavu da kewaye a lardin Kivu ta Kudu, a gaɓar tafkin Kivu da kusa da kan iyaka da Rwanda .[3] Kafofin yaɗa labarai na cikin gida sun ruwaito cewa an lalata gidaje da hanyoyi da ababen hawa. Ruwan mai ƙarfi ya kwashe motoci tare da jefa su cikin tafkin Kivu . Ɗaya daga cikin yankunan da lamarin ya fi shafa shi ne ƙaramar hukumar Kadutu . [4] An kashe mutane 10 tare da lalata daruruwan gidaje.[5]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Powerful flood waters swept away cars and dumped them into Lake Kivu Bukavu Congo (in Turanci), retrieved 2022-04-12
- ↑ "Four children among six dead in DR Congo deluge". sharjah24. 22 February 2022.
- ↑ "DRC: Disruptions due to flooding ongoing in Bukavu, South Kivu Province, as of March 18". DRC: Disruptions due to flooding ongoing in Bukavu, South Kivu Province, as of March 18 | Crisis24 (in Turanci). Retrieved 2022-04-12.
- ↑ "DR Congo – Deadly Floods in South Kivu Province – FloodList". floodlist.com. Retrieved 2022-04-12.
- ↑ "Ten killed in Bukavu floods". The New Humanitarian (in Turanci). 2000-05-31. Retrieved 2022-04-12.