Ambaliyar Ruwa a Kinshasa, 2022
A ranakun 12 zuwa 13 ga watan Disambar 2022,[1] ruwan sama kamar da bakin kwarya ya bar tituna, ababen more rayuwa da kuma unguwanni da dama a ƙarƙashin ruwa ko kuma sun lalace a Kinshasa, babban birnin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.
Iri | aukuwa |
---|---|
Kwanan watan | 13 Disamba 2022 |
Ƙasa | Jamhuriyar dimokuradiyya Kwango |
Tasiri
gyara sasheHanyoyi da dama a tsakiyar birnin Kinshasa sun nutse yayin da aka shafe sa'o'i ana sheƙa ruwan sama kamar da bakin ƙwarya tare da rushewar gidaje da dama. [2] A ƙalla mutane 169 ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa. [3] Yawancin waɗanda suka mutun dai na faruwa ne sakamakon zaftarewar ƙasa sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya. [2] A ƙalla gidaje 280 ne suka ruguje yayin da wasu sama da 38,000 ambaliyar ruwa ta shafa. [4] Mutane miliyan 12 da suka ƙunshi galibin mutanen birnin ne ambaliyar ruwa ta shafa.[5]
Bayan haka
gyara sasheGwamnatin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kwango ta sanar da gudanar da zaman makoki na kwanaki uku a ƙasar .[2]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "DR Congo: Floods and Landslides - Dec 2022". ReliefWeb. 15 December 2022.
- ↑ 2.0 2.1 2.2 "DR Congo floods leave more than 120 dead in Kinshasa". BBC News. 14 December 2022.
- ↑ Dorian Geiger (17 December 2022). "At least 169 dead after devastating floods in DR Congo's Kinshasa". Al Jazeera.
- ↑ "Landslides kill 141 in Congo". Radio Pakistan. 14 December 2022. Archived from the original on 16 December 2022. Retrieved 7 May 2023.
- ↑ "Floods and landslides kill scores of people in Kinshasa". The Guardian. 14 December 2022.