Almara labari ne, ko tambaya ta sigar wasa kwakwalwa, angambo ya bayyana Almara da labarin da ke jefa tambaya a cikin kwakwalwan mai saurare.[1]

Almara zance ne wanda hausawa sukeyi alokacin nishadi ko kuma wasa kwakwalwa.

Rabe-Raben Almara

gyara sashe

A dunkule, masana harshen Hausa sun kasa almara zuwa gida biyu:

  1. Almarar Wasa kwakwalwa: ita ce almarar da ke dauke da labarin da ke dauke da matsalar da bayan an gama bayar da shi za a bukaci masu sauraro su warware matsalar. Misali, wata rana, wata budurwa ta je zance wajen saurayinta da ya ke wani gari. Da suka gama zance, dare ya yi, sai ya tafi zai raka ta. A tsakanin wadannan garuruwa guda biyu, akwai wani kogi. Da suka isa bakin wannan kogi, sai saurayin ya ce budurwar ta dakata, ya iya ruwa, shi zai fara haura kogin ya dauko kwale-kwale don ya haye da ita. Sai ya shiga ruwa, sai da ya je tsakiyar ruwan, sai wani katon kada ya biyo shi zai kama shi, da kyar ya samu ya haye. Bayan ya haye, sai ya hango kura ta rugo da gudu za ta cinye wannan budurwar tasa. To, wai idan kai ne wannan saurayin ya zaka yi? Za ka shigo ruwa kada ya cinye ka ne, ko kuwa za ka tsaya kura ta cinye budurwar taka?
  2. Almarar Raha: almara ce da ake yin ta ta hanyar bayar da labarin bandariya, wacce kuma ba ta dauke da wata matsalar da a karshe za a nemi mai sauraro ya warware ta.

Akwai kamanceceniya tsakanin almara da tatsuniya. Sai dai, babban abin da ke bambanta tsakaninsu su shi ne cewa, an fi gina almara da sunayen mutane, wato ba a cika gina zunzurutun labarin almara da sunayen wasu halittu zalla ba batare da mutum ya shigo ciki ba.

  • Furniss, Graham. (1996). Poetry, prose and popular culture in Hausa. International African Institute. Edinburgh: Edinburgh University Press for the International African Institute. ISBN 978-1-4744-6829-9. OCLC 648578425.
  • ·Warfare in the Sokoto Caliphate : historical and sociological perspectivesISBN0-521-21069-0OCLC2371710
  • ·The Sokoto Caliphate : history and legacies, 1804-2004. Bobboyi, H., Yakubu, Mahmood. (1st ed ed.). Kaduna, Nigeria: Arewa House. 2006. ISBN 978-135-166-7. OCLC 156890366.

Manazarta

gyara sashe
  1. Furniss,Graham. (1996). Poetry,prose and popular culture in Hausa.p.57