Aliyu isa nata
Aliyu Isah Nata mawaki ne haifaaffen jihar katsina,fasihin mawaki ne Kuma matashi wanda yake da masoya a sassan Nijeriya gaba daya.
Rayuwar sa
gyara sasheAn haifi Aliyu a cikin garin katsina anan ya girma yayi karatun sa tun daga matakin firamare zuwa sakandiri har kwalejin, yayi firamare a kofar ruwa firamare school sannan yai sakandiri a Gdss Ahmad Mubarak sakandiri school , daga Nan ya shiga kwalejin horar da malamai ta jihar katsina anan ya Yi NCE.
Fara waka
gyara sasheAliyu yace tun yana karami yake da burin yin Waka domin ya isar da sako ga duniya, wakar da ta fito dashi itace wakar AURE MARTABA.daga nan yai wakoki da dama.
Daukakar sa
gyara sasheAliyu yayi wakokin da dama Amma yace sanadin daukakarsa ita ce wakar da yayi ta AURE MARTABA. Da sauran fitattun wakokin sa da yayi.
Aure
gyara sasheyayi aure a shekarar 2021 a watan ugusta 21 ga watan sunan amaryarsa ZAINAB SULAIMAN, a yanzun haka ta haihu inda ta Haifa masa yaro namiji sunan yaron MUHAMMAD ALIYU ISA NATA. Suna zaune cikin aminci .
wakokin sa
gyara sashe- Ummanah
- Asma,u diyar Abu total
- Zainabu abuwa
- Aure MARTABA
- Dare namiji aure
- godiya
- Ina sonki
- dadin rayuwa
- Hayatu mu,azu
- habu sarki
- Aishatul humaira
- Bege
- Dan sanda
- Hayatu mu,azu
Manazarta
gyara sashe- ↑ https://www.dw.com/ha/tarihin-mawaki-aliyu-haidar-da-tasirin-baitukan-wakokinsa/av-56807992https://fimmagazine.com/me-ya-sa-mawa%C6%99i-aliyu-nata-ya-yi-kuka-a-lokacin-bikin-auren-sa-da-zee-fulani/
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-11. Retrieved 2023-07-11.
- ↑ https://www.dw.com/ha/tarihin-mawaki-aliyu-haidar-da-tasirin-baitukan-wakokinsa/av-56807992