Aliou Badara Baldé (an haife shi 12 ga watan Disambar 2002) ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne kuma ɗan ƙasar Senegal wanda ke taka leda a matsayin winger kulob ɗin FC Lausanne-Sport na Switzerland.

Aliou Balde
Rayuwa
Haihuwa Ziguinchor (en) Fassara, 12 Disamba 2002 (21 shekaru)
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
 

Aikin kulob gyara sashe

A ranar 19 ga watan Janairun 2021, Baldé ya sanya hannu kan kwangilar ƙwararru tare da Feyenoord.[1] Ya fara wasansa na farko tare da Feyenoord a wasan 1-1 Eredivisie da FC Emmen a ranar 20 ga watan Maris ɗin 2021.[2]

A ranar 7 ga watan Janairun 2022, an bada Baldé aro ga Waasland-Beveren a Belgium.[3] A ranar 31 ga watan Agustan 2022, an bada shi aro zuwa Dordrecht.[4] A ranar 31 ga watan Janairun 2023, an sake kiran Baldé daga lamunin da ya yi a FC Dordrecht kuma ya koma kulob ɗin Swiss FC Lausanne-Sport.[5]

Ayyukan ƙasa da ƙasa gyara sashe

Baldé ya wakilci Senegal U17s a gasar cin kofin duniya ta FIFA U-17 na 2019.[6]

Manazarta gyara sashe

  1. https://www.feyenoord.nl/nieuws/nieuwsoverzicht/feyenoord-contracteert-senegalees-talent-aliou-balde-190121
  2. https://int.soccerway.com/matches/2021/03/20/netherlands/eredivisie/feyenoord-rotterdam-nv/fc-emmen/3304729/
  3. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2022-01-10. Retrieved 2023-03-20.
  4. https://fcdordrecht.nl/2022/08/31/30632/
  5. https://www.vi.nl/cookies/;jsessionid=005A79B9CDCD7B4E447934068F5FE23A
  6. https://wiwsport.com/2019/10/13/diambars-aliou-badara-balde-parmi-les-60-meilleurs-u17-de-la-planete/