Ali bin Mohsen bin Fetais Al-Marri An haife shi a ranar 8 ga watan Fabrairu, shekara ta 1965, a Doha) babban jami'in kasar Qatari ne kuma majistare.

Ali bin Fetais Al-Marri
Rayuwa
Haihuwa Doha, 8 ga Faburairu, 1965 (59 shekaru)
ƙasa Qatar
Karatu
Harsuna Larabci
Sana'a
Sana'a Lauya da civil servant (en) Fassara

Ya kasance Babban Lauyana kasar Qatar a shekara ta alif dubu biyu da biyu 2002 zuwa shekara ta alif dubu biyu da a shirin da daya 2021.

Ali Bin Fetais Al-Marri shi ke rike da Ofishin Majalisar Dinkin Duniya kan Magunguna da Laifuka na Musamman kan magan ce Cin Hanci da Rashawa.[1]

Shi ne wanda ya kafa Cibiyar Shari'a da Cin Hanci da rashawa (ROLACC), wanda aka ƙaddamar a Doha a shekara ta alif dubu biyu da goma sha biyu 2012 kuma tsohon Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon ne ya kaddamar da shi.[2]

Tarihin rayuwar shi

gyara sashe

An haife shi a ranar 8 ga watan Fabrairu, shekara ta 1965, a Doha, Ali Bin Fetais Al-Marri ya samo asali ne daga kabilar Bedouin Al-Marris .

Bayan kammala karatunsa a kasar Qatar, Ali Bin Fetais Al-Marri ya samu kammala digiri sa na biyu a fannin Shari'ar a Jami'ar Rennes, Faransa, kuma ya samu kammala PhD a bangaran Shari'ar na Kasa da Kasa, a Jami'ar Sorbonne, Faransa, a shekara ta 1997,

Ali Bin Fetais Al-Marri yana magana da kusan yare ukku Larabci da Faransanci da kuma turanci .[3]

Ali Bin Fetais Al-Marri ya yi aure kuma yana da 'ya'ya maza biyu.

Ayyukan sana'a

gyara sashe

Jami'ar Qatar

gyara sashe

Ali Bin Fetais Al-Marri ya fara aikinsa a shekarar 1997 a matsayin mataimakin farfesa a Jami'ar kasar Qatar, inda ya koyar da dokar kasa da kasa.

Majalisar Ministoci

gyara sashe

A shekara ta 1997, an nada shi Mataimakin Sakatare Janar na Majalisar Ministoci kuma ya halarci tarurruka na mako-mako.

Diwan na Sarkin sarakuna

gyara sashe

Daga shekara ta 1998, ya jagoranci sashen shari'a na Diwan na Sarkin Qatar, a matsayin Mataimakin Sakatare.

A watan Maris na shekara ta alif dubu biyu da daya 2001, Ali Bin Fetais Al-Marri ya wakilci Qatar a gaban Kotun Shari'a ta Duniya a cikin shari'ar iyakokin teku da batutuwan yankin tsakanin kasar Qatar da Bahrain. [4]

Babban Lauyan

gyara sashe

An nada Ali Bin Fetais Al-Marri a matsayin Babban Lauyan Qatar ta hanyar dokar Sarkin a ranar 19 ga watan Yuni, shekara ta alif dubu biyu da biyu 2002.

Majalisar Dinkin Duniya

gyara sashe
 
Dokta Al Marri yana halartar wani taron gida a Doha, Qatar

Ali Bin Fetais Al-Marri ya kasance memba na Hukumar Shari'a ta Duniya a Majalisar Dinkin Duniya tun a shekara ta alif dubu biyu da biyu 2002. A watan Satumbar shekara ta alif dubu biyu da goma sha biyu 2012, an nada shi wakilin yanki na musamman na Ofishin Majalisar Dinkin Duniya kan Magunguna da Laifi (UNODC) dan dawo da kadarorin da aka sace. Ayyukansa sun haɗa da tallafawa ayyukan da suka shafi haɓaka dabarun ƙasa da ƙasa don dawo da kudaden sata, ba da shawara, da kuma ba da gudummawa ga ma'anar ayyukan haɓaka ƙwarewa da taimakon fasaha don kafa tsarin ƙasa don dawowa da kuɗi da hana ƙuntataccen gudummawar kuɗi, da haɓaka taimakon shari'a.

An sabunta wa'adinsa a cikin a shekara ta alif dubu biyu da goma sha hudu 2014, kuma an cire sunansa a cikin masu ba da shawara na Musamman a Majalisar Dinkin Duniya kan Rigakafin Cin Hanci da rashawa . Tun daga wannan lokacin, Dokta Ali bin Fetais ya ba da gudummawa da kiran rage cin hanci da rashawa a cibiyoyin gwamnati da ilimi.[5]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Division for Peace Advisory Board". UNITAR (in Turanci). Retrieved 2021-04-02.
  2. "The Rule of Law and Anti-Corruption Centre launched in Qatar". Subject to Inquiry (in Turanci). 2011-12-12. Retrieved 2020-08-25.
  3. "CV" (PDF). Archived from the original (PDF) on 2018-08-15. Retrieved 2018-06-10.
  4. "International Court of Justice" (PDF). Archived from the original (PDF) on 2018-08-15.
  5. "H.E. Dr. Ali Bin Fetais Al-Marri". UNITAR (in Turanci). Retrieved 2021-04-07.