Hausawa suna da al'adu masu bada sha'awa idan aka zo batun aure.

-Duk da Musulunci ya canja al'adu da dama na auren Bahaushe.

-Amma a fagen birgewa da kayatarwa auren Hausawa ya ciri tuta.

Al'adu na biyo bayan ɗaurin aure a musulunci.

Akwai tabbacin mutane da dama sunyi ta ganin hotunan bikin auren Hausawa, kuma an yi ta burin sanin yadda al'ada ta tanada.

A nan zamu kawo muku yadda Hausawa suke da al'adunsu masu ban sha'awa idan shagalin aure ya tashi. Ana fara yin wasu al'adu kafin ɗaurin aure, wasu al'adun kuma suna biyo bayan daurin aure.

1.Kayan Zance

Sune kayan da dangin saurayi ke gabatarwa ga dangin budurwa da yake son ya aura dan kowa yasan yana neman aurenta.

Abubuwan da zasu kawo sun hada da kayan kicin,kayan kwalliya,takalma, kudin gaisuwa da makamantansu.

Idan dangin angon suna da hali ,akan bukaci su bayar da gidan da mijin zai ajiye matarsa .Idan hakan ta faru,wajibi ne dangin amarya suyi mata duk wasu kayan daki,falo,da kuma kicin.

Anayin duk wadannan abubuwan ne kafin daurin aure.

2. Daurin Aure

Shafa Fatiha tafi komai muhimmanci a gaba daya sha'anin.Hausawa da dama su kan bayyanar da wakilin ango daga dangi ko 'yan uwa daabokan arzikinsa. Kuma wannan auren baya tabbata har sai an samu waliyin amarya. Wannan waliyin shineh wanda zai yi jagoranchi a matsayin mai tsaya ma amarya a rayuwar auran ta

Sai Limami wanda shi zai daura auren sannan ya gabatar da addu'o'in zaman lafiya ga ma'auratan .Ana yin haka ne kamar yadda addini ya tanadar.

3. Sa Lalle

Mata ne kadai ke yin wannan. Shine lokacin da amarya ke samun damar hira da kawayenta hade da barkwanci,a gidan mahaifinta.

Ana kwaba lalle don ayi wa amarya ado da kawayenta ado na musamman a hannayensu da kafafu.

Amma dole ne lallen amarya ya banbanta da na kowa a wurin yawa da kyau musamman na hannayenta. Hakane na biyo bayan ciye-ciye da kawayen amarya da amarya zasu yi. Sa lalle a wanna zamanin namu ya chanza salo inda yanxu ake anfani da turare a maimakon anfani da lalle inda ake feshe amarya tare da kawayenta

4. Kamun Amarya

Kamu dadaddiyar al'adar hausawa ce.Kuma tana daukan hankalin jama'a da dama.Ana ciniki ne tsakanin dangin Ango da Amarya don a sakar masu amaryarsu.

Kudin da dangin Ango zasu bayar ya danganta da yanayin arzikinsu.Anayin cinikin cikin nishadi da barkwanci na tsawon minti talatin '30' tukunna a ci a sha.

5.Kai Amarya

Ana kai amarya ta hanyoyi guda uku, na farko shineh wanda baban amarya zai kai amarya har dakin mijinta, sai na biyu wanda abokan ango tare da kawayen amarya da wasu daka cikin dangin amarya da ango zasu kai amarya, sai na uku shineh wanda ango dakanshi zaizo yadau amarya da kansa yakaita gidansa. Amma dai anfi anfani da na biyu a wannan lokacin. Kuma akwai wani abinchi da al'adar hausa akeyi daga gidan ango a kawo gidansu amarya kafin daukan amarya wanda ake kiranshi kabaki.

Wannan bashi bane karshen al'adun hausawa ba a wurin bikin aure ba.

Duk da dai ya danganta da arzikin danginsu,tun da ana gabatar da kayan ciye-ciye,kade-kade, da kuma nishadi.

6.Siyan Baki

A wasu wuraren, akanyi al'adar nan don ta karawa bikin armashi.Siyan baki wata al'ada ce wadda za'ayi ciniki tsakanin abokan Ango da kawayen

amarya kafin subar ango y gana da amaryarsa.

Manazarta

gyara sashe

https://hausa.legit.ng/1372335-auren-hausawa-dukkan-abinda-ya-kamata-a-sani-daga-nema-zuwa-samun-auren.html