Aisha Najamu
Aisha Najamu, jaruma ce a masana'antar fim ta Hausa wato kanniwud. tana ɗaya daga cikin kyawawan mata a masana'antar, tayi fice ne a shahararren fim mai dogon zango wato Izzar so, jaruma ce data kware a acting, ta Kuma fito a shahararren fim din Nan, Mai suna kishiyata, da kuma Sarauta.[1]tana fitowa a wakokin soyayya.
Takaitaccen Tarihin ta.
gyara sasheAisha Izzar so(hajiya nafisa) Cikakken sunan ta shine Aisha najamu , an haifeta a ranar 12 ga watan ugusta shekarar 1997,ta tashi tare da iyayenta da Yan uwa a cikin jihar kano, tayi karatun firamare da sakandiri a garin Kano,bayan ta gama SE ta tafi jami'ar Maiduguri ta cigaba da karatun ta, Haifaffiyar jihar jigawa ce tayi karatun firamare da sakandiri a garin jigawa daganna ta wuce Jami'ar Maiduguri inda ta Karanci kasuwanci,baban su Yana ma yaran sa auren wuri tayi aure inda ta haifi Yara Yan biyu tun tana yarinyar ta, a yanzun haka Bata da aure,[2]