Aikin Olympic don 'Yancin Dan Adam
Aikin Olympics don yancin ɗan adam (OPHR) ta kasance ƙungiya ce ta Amurka wacce wani masanin zamantakewa mai suna Harry Edwards da sauransu suka kafa, gami da fitattun 'yan wasan Olympics da suka hada da Tommie Smith da John Carlos, a cikin watan Oktoban 1967. Manufar kungiyar ita ce yin zanga-zangar adawa da wariyar launin fata a Amurka da sauran wurare (kamar Afirka ta Kudu), da kuma wariyar launin fata a cikin wasanni gaba daya.[1]
Aikin Olympic don 'Yancin Dan Adam | |
---|---|
Bayanai | |
Iri | non-governmental organization (en) |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 1967 |
Smith ya ce aikin ya shafi 'yancin ɗan adam, da "dukkan nin bil'adama."[2]Yawancin membobin OPHR sun kasance 'yan wasan Amurka ne da wasu daga cikin Afirka san nan da wasu shugabannin al'umma.
Fage
gyara sasheA tsakiyar karni na 20 wasanni a Amurka an yi amfani da su don nuna cewa akwai ƙarancin wariyar launin fata na hukumomi fiye da yadda ake yi. A cikin wata hira da Vox, Dexter Blackman, farfesa a bangaren tarihi a Jami'ar Jihar Morgan, ya ce: "Kafofin watsa labarai sun fara tallata baƙar fata 'yan wasa a matsayin alamar cewa dimokuradiyyar launin fata ta wanzu a Amurka ... wani abu da aka yi amfani da shi don yin watsi da shi. tambaya game da wariyar launin fata da aka kafa". Wannan ya zama ruwan dare tun kafin a soke wariyar doka a Amurka a hukumance[3]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Resistance: the best Olympic spirit – International Socialism" (in Turanci). Retrieved 2019-05-29.
- ↑ Silent Gesture – Autobiography of Tommie Smith (excerpt via Google Books) – Smith, Tommie & Steele, David, Temple University Press, 2007, 08033994793.ABA
- ↑ "The story behind this iconic Olympics protest". Youtube. Vox Media. Retrieved 2020-07-13.