Ahmad Suleiman Ibrahim wanda akafi sani da Alaramma Ahmad Suleiman (an haifesh a shekara ta 1966) makaranci ne najeriya,malamin musulunci,limami,sannan kuma yayi fice wajen karatun alkuráni,sannan kuma ya karbi kyaututtuka a dunia gabadaya,saboda inghancin shi wajen karatun alkuráni.[1]

Farkon rayuwa gyara sashe

An haifi Ahmad Suleiman a cikin zuriár Suleiman,wanda baban sa ya rasu tun yana shekara shida a duniya, inda ya koma jahar kano yana dan shekara tara domin yin karatun musulunci da kuma karatun zamani.Ahmad Suleiman ya haddace alkuráni tun a farkon rayuwarsa ya kuma fadi cewa Dakta Kabir Haruna Gombe na daga cikin malaman da suka koyar dashi,sannan kuma ya zamo alaramman sa a lokacin tafsirin ramadan.Ahmad suleiman memba ne a kungiyar izala wadda itace kungioya mafi girma dake yawo a najeriya.

Garkuwa gyara sashe

A cikin watan maris na shekarar 2019,wasun masu garkuwa da mutane sun sace Sheikh Amahd Suleiman a hanyar sa ta dawowa gida bayan ya kai ziyar a jahar kebbi.An ruwaito wasu ýan bindiga da baásan su ba sun sace Ahmad Suleiman a jahar katsina,kafofin mabanbanta,sun tabbatar da cewa an sace Ahmad Suleiman ne tare da wasu mutane guda biyar daga hanyar sheme zuwa karamar hukumar kankara dake jihar katsina.[2][3][4][5] An saki Sheikh bayan kwana sha biyar da daukeshi.[6][7][8][9]

Gwamnan Jahar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya nada Sheikh Ahmad Suleiman a matsayin kwamishinan ilimi na jahar kano.[10] [11]

Manazarta gyara sashe

  1. https://dawahnigeria.com/dawahcast/a/1560
  2. https://www.vanguardngr.com/2019/03/kidnappers-of-buharis-prayer-warrior-sheikh-sulaiman-demand-n300m-ransom/amp/
  3. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2022-01-17. Retrieved 2023-03-13.
  4. https://prnigeria.com/2019/03/19/sheikh-suleiman-kidnappers-ransom/
  5. https://guardian.ng/news/kano-islamic-clergy-five-others-kidnapped/
  6. https://guardian.ng/news/sheikh-ahmad-sulaiman-regains-freedom-after-15-days-in-captivity/
  7. https://www.channelstv.com/2019/03/27/famous-kano-sheikh-five-others-regain-freedom-after-13-days-in-kidnappers-den/
  8. https://www.bbc.com/news/world-africa-48435964
  9. https://www.premiumtimesng.com/news/top-news/321015-kidnappers-of-buharis-prayer-warrior-demand-n300m-ransom.html?tztc=1
  10. https://hausa.legit.ng/news/1446128-labari-cikin-hotuna-ganduje-ya-nada-alaramma-ahmad-sulaiman-kwamishinan-ilimi-2/
  11. https://hausa.legit.ng/news/1446478-hotuna-cikin-labari-alaramma-ahmad-sulaiman-ya-shiga-ofis-ya-mika-godiya-ga-allah/