Ahmad Shanawa
Ahmad Shanawa(Baban chakwai)
Jarumi ne a masana antar fim ta Hausa wato kanniwud Kuma mawaki fitaccen mawaki shahararren mawaki yayi Wakoki da dama a masana antar. Ahmad ja[1]rumi ne na barkwanci Kuma mawaki sannan kuma shine babban darakta na kamfanin B Record.[2]
Takaitaccen Tarihin Sa
gyara sasheAhmad Shanawa inkiyan da ake masa kenan, ana Kiran sa da suna Baban chakwai ne saboda shi ye wakan" kamas,bawan mata, chakwai" da sauran su. Ahmad mawakin Hausa ne da Kuma gambara wato hip hop da wasan barkwanci, sannan Ahmad ya fito a fina finai da dama wadanda akayi a garin Jos . Ahmad Haifaaffen jihar filato ne garin Jos yayi karatun sa gaba daya a garin Jos, daga Nan ya fara bidiyon wasan barkwanci da Kuma wakokin Hausa, yayi wakar baby chakwai Wanda daga Nan ake Kiran sa da baban chakwai,
An fara sanin sa ne daga sadda yai wakar baby chakwai da Kuma wakar siyasa da yayi ma shugaban kasa baba buhari Mai suna"APC SAK" daga Nan ya shahara yayi wakan a shekarar 2017.se Kuma ya Kara daukaka da yayi wakar kamas da wakar bawan mata a 2018. Ahmad nada mata daya da yarinya mace daya.
Wakokin sa
- Bawan mata
- Chakwai
- Kamas
- Gaskiya
- APC SAK
- corona
- Kiyafe ni
- Soja mazan fama
- inason mata
- Kamar da wasa
- maya
- dan makaranta
- Garin masoyi[3]
- ↑ https://hausatutoblog.blogspot.com/2018/11/kalaman-ahmad-shanawa-ga-yarsa-ranar.html?m=1
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-29. Retrieved 2023-07-29.
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-29. Retrieved 2023-07-29.