Ahmad Rufa'i Dan Shehu Dan Fodio

Ahmad Rufa'i Dan Shehu Dan Fodio (Haihuwa da Rasuwa: 1810 zuwa 1873). An kuma haife shi a cikin tsakiyar yaki, hakan yasa ya bude ido sosae da lamarin yaki, tun yana dan yaransa mutane ke daraja shi domin dabi’unsa da su kai daidai da na Shehu da kuma tsakanin soyayyarsa da ilimi da karatu.Mutane dayawa suna kwatantashi da Shehu wajen kamanni. Ya kuma kasance lokacin mulkinsa yana da tsanani akan barayi da masu laifi ko wani iri. Kuma mai tsanani ne akan bin doka da oda kan dukkan mabiyansa.[1]

Karatu gyara sashe

Kamar yadda al’adar gidan Shehu take Ahmadu shima ya taso ne bisa kula na mahaifinsa akan karatun tukanshi da tarbiyyansa. Duk da basu ɗauki lokaci mai tsawo ba mahaifin nashi ya rasu. Hakan yasa Ahmadu yayi karatu ne a wajen Malamai wa inda suke taya mahaifin nashi aiki. Muhammad Bello da Abubakar Atiku, su suka cigaba da kula da karatun yaran Shehu bayan Allah yayiwa shehun rasuwa.[1]

Sarauta gyara sashe

Ahmadu Rufa’i yayi shekaru kafin samun sarautarsa, inda aka nada shi a matsayin Kalifa a Masallacin Wurno a watan october 18th, bayan kwana biyar da mutuwar wanda ya gada a wajen sa shine Aliyu Karami.[1]

Rasuwa gyara sashe

An kuma ruwaito cewa Ahmadu Rufa’i yayi mulki na tsawon shekara biyar (5) da wata shida (6) da kwana ashirin da uku (23). Ya rasu a gida kusa da gidan mahaifinsa a ranar 10 ga watan Mayu (March), a shekarar alif

Bibiliyo gyara sashe

  • Bobboyi, H., Yakubu, Mahmud.(2006). The Sokoto Caliphate: history and legacies, 1804-2004, 1st Ed. Kaduna, Nigeria:Arewa House. ISBN 978-135-166-7
  • Hamman, Mahmoud, 1950- (2007). The Middle Benue region and the Sokoto Jihad, 1812-1869 : the impact of the establishment of the Emirate of Muri. Kaduna: Arewa House, Ahmadu Bello University. ISBN 978-125-085-2. OCLC 238787986.
  • Usman Muhammad Bugaje. The Tradition of Tajdeed in West Africa: An Overview International Seminar on Intellectual Tradition in the Sokoto Caliphate & Borno. Center for Islamic Studies, University of Sokoto (June 1987)
  • Hugh A.S. Johnston . Fulani Empire of Sokoto. Oxford: 1967. ISBN 0-19-215428-1.
  • S. J. Hogben and A. H. M. Kirk-Greene, The Emirates of Northern Nigeria, Oxford: 1966.
  • Kabir, Hajara Muhammad,. Northern women development. [Nigeria]. ISBN 978-978-906-469-4. OCLC 890820657.

Manazarta gyara sashe

  1. 1.0 1.1 1.2 Kabir,Hajara Muhammad,. Northern women development. [Nigeria].p.p 133-144 ISBN 978-978-906-469-4. OCLC 890820657.