Alhaji Ahmad Mai Deribe da a kafisani da fadar Mai deribe. Gidane da yashiga kundin tarihin duniya. Sakamakon yadda a ka cudanya ruwan zinari wajen gina wasu sassan gidan. Taf keken gidane da ke kunshe da sassa daban daban, inda yake da manyan sassa biyar, da suka kunshi shashen me gida da na matansa hudu. Shine gida mafi tsada kuma mafi. kyau a Nahiyar Afirica, alokacin da a ka ginashi.[1] Sannan yana cikin manyan wurare ashirin, na duniya masu burgewa. Gidan yajawo hankalin mutane daga sassa daban daban na duniya zuwa maiduguri. Fadar deribe ta karbi ba kuncin mai martaba sarki juan carlos na spain wanda ya kwana biyu a gidan a alif dari tara da tamanin da shida. Wanda kuma bayan ziyartar gidan ya bayyana cewa al'ummar Borno suna da tarihin fasahar zanen gidaje a kasar Spain  tun shekara dubu da suka gabata. Harwayau Gidan yakarbi bakuncin yarima Charles NA ingila da matarsa marigayiya Gimbiya Diana. Da tsohon shugaban Amurka George w. Bush.  Da tsohon firayiministan Kanada. Da Sauran fitattun mutanen duniya . Gidan tamkar shine taj-mahal din mutanen borno da najeriya, da kuma Africa. Anfara aikin gidanne a farkon shekaran Alif dari Tara da  tamanin. Inda a ka Gina shi a wani katafaren fili. kadaje da kujerun da a kazuba a Gidan wani camfani ne mesuna Giovanni monzio compagnoni (GMC) dake kasar italiya yayisu. Wannan companion yasamar wa attajiran mutanen kayayyakin Gida. Irinsu marigayi sarki fahad bin Abdul-azis NA saudiya da Omar bongo shugaban kasar  Gabon. Da sultan Kaboos bin sa'id. NA Oman. Da Sheikh khalifa Alnahayan NA UAE.

Manazarta

gyara sashe
  1. https://www.thisdaylive.com/index.php/2019/08/18/oil-businessman-alhaji-zanna-mai-deribes-headache/