Ageing
Tsufa (Ageing a cikin Ingilishi na amurka).A faffadar ma’ana, tsufa na nufin sel guda daya a cikin kwayoyin halitta wadanda suka daina rarrabuwa, ko kuma ga yawan nau’in jinsin. A cikin mutane, tsufa yana wakiltar tarin canje-canje a cikin dan adam akan lokaci kuma yana iya hadawa da canje-canjen jiki, tunani, da zamantakewa.Lokacin amsawa, alal misali, na iya raguwa tare da tsufa, yayin da tunani da ilimin gabadaya ke raguwa. Tsufa yana da alaka da kara hadarin cutar kansa, cutar Alzheimer, ciwon sukari, cututtukan zuciya, kara hadarin lafiyar kwakwalwa, da kari mai yawa.A cikin kusan mutane 150,000 da ke mutuwa kowace rana a fadin duniya, kusan kashi biyu bisa uku na mutuwa daga dalilai masu alaka da shekaru. An danganta wasu zabin salon rayuwa da yanayin zamantakewar al'umma da tsufa. An ba da ka'idodin tsufa na yanzu zuwa ra'ayi na lalacewa, ta yadda tarin lalacewa (kamar DNA oxidation) na iya haifar da tsarin ilimin halitta yai kasa, ko kuma ga tsarin da aka tsara na tsufa, ta hanyar tsarin ciki (kyautawar epigenetic kamar DNA methylation) a zahiri na iya haifar da tsufa. Tsarin tsufa bai kamata a rikita shi da tsarin mutuwar kwayar halitta ba (apoptosis).
ageing | |
---|---|
biological process (en) da failure mode (en) | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | developmental process (en) , degradation (en) da senescence (en) |
Bangare na | developmental process (en) |
Has cause (en) | increase (en) |
Karatun ta | ageing research (en) da gerontology (en) |
Has characteristic (en) | Hallmarks of aging (en) |
manazarta
gyara sashe1:https://www.ncbi.nlm.nih.gov/pmc/articles/PMC4712935 2:https://www.nia.nih.gov/about/aging-strategic-directions-research/understanding-dynamics-aging 3:https://www.ncbi.nlm.nih.gov/pmc/articles/PMC5316899 4:https://doi.org/10.5493%2Fwjem.v7.i1.1 5:https://slate.com/technology/2020/03/aging-disease-classification.html