Adolf Hitler (An haifishi ranar 20 ga watan Afrilu a shekara 1889) a birnin Braunau a cikin ƙasar Austria dake tsakiyar Turai. Hitler ɗan siyasa ne kuma ɗan mulkin kama karya ne. Tun daga shekara 1921 shi shugaban jam'iyyar NSDAP, jamiyar mai tsanani, ne. A shekarar 1933 ya zama shugaban gwamnati, a shekara 1934 shi ma ya zama babban shugaban ƙasar Jamus har kisan kansa a shekara 1945.[1][2]
Adolf yana gabatar da jawabi a yayin wani taro a Danzig
A cikin lokacin gwamnatinsa jam'iyyar NSDAP ta kafa mulkin kama karya mai sunan "Daula ta Uku". A cikin shekara 1933 an hana dukan sauran jam'iyyoyii sai jam'iyya ta Hitler. An zalunci abokan hamayya don jifansu a kurkuku ko sansu a sansanin gwale-gwale, inda an yi musu azaba aka kashe su. Hitler dai mai nauyi ne game da kisan gillar Yahudawa na Turai da kashin mutanen da yawa don dalilan na adini da na ƙabila da kuma na zaman jama'a. Siyasar ta shugabancin Hitler sanadi cee ga ƙaddamarwa da yaƙin duniya na biyu, a cikinsa mutane milyon da dama da kuwa yankunan da yawa suka halaka.[3]