DAGA CIKIN ADDU'O'IN ANNABI (SAW) A SUJJADA

Nana Aisha رضي الله عنها ta ce: "Na (farka) a wani dare na nemi Manzon Allah صلى الله عليه وسلم, sai ban gan shi a shimfida ba. Da na lalube shi, sai hannuna ya fada bisa cikin tafin kafafunsa a masallaci (wato yana sallah), ya kafe su (a irin yanayin mai sujjada) yana cewa:

"اللهم اعوذ برضاك من سخطك، وبمعافاتك من عقوبتك، واعوذ بك منك، لا احصى ثناء عليك، أنت كما اثنيت على نفسك."

Ma'ana: Ina neman tsari da yardarka daga fushinka, da afuwar ka (don samun kariya) daga ukubar ka. Ina neman tsari da kai daga (afkawa cikin fushin) ka. Ba zan iya kididdige yabo gare ka ba. Hakika kai ka kasance ne kamar yadda ka yi yabo ga kanka."

             Muslim:486