Adam M Adam Tsohon jarumi ne a masana'antar fim ta Hausa wato kanniwud Wanda har yanzun ake damawa dashi , ya Dade Yana fim da dadewa.[1]

Takaitaccen Tarihin Sa

gyara sashe

Adam Haifaffen garin Kano ne a Karamar hukumar gwale yayi karatun firamare a gwale firamare school yayi sakandiri a gwale sakandiri school, daga Nan ya tafi FCE KANO inda yai karatun difloma anan ya tsaya. Bayan ya gama difloma ya fada harkan fim inda a yau ya kwashe tsaawon shekara 25 zuwa 26 a masana antar. Ya shigo masana'antar ne bayan ya gama firamare ya koma Lagos gurin kanin mahaifiyar sa ,Yana zuwa yaje ya dawo Kano , acan Lagos Yana kallon fina finan Hausa na wancan lokacin ,sadda Yana makaranta ya rubuta Wani littafi Mai suna Mai gaskiya, ya kaima ado Ahmad gidan dabino littafin domin yai mishi gyara a Kuma buga littafin, bayan anyi haka SE yace Bara Shima yayi fim mana , tunda Yana da kudi a ka Maida littafin fim mai suna Mai gaskiya shi yazama fim din sa na farko a masana'antar daga Nan ya cigaba da fim yayi fina finai da dama a masana'antar.

  • Mai gaskiya
  • Bazawara
  • Talala
  • Fati mukhtar
  • Kona gari[2]

Manazarta

gyara sashe