alif

Abubakar Uba Galadima (An haife shi ranar 17 ga watan Agusta, shekara ta alif ɗari tara da sittin da biyar 1965) miladiyya. a garin Kuki dake karamar hukumar Bebeji a jihar Kano.

Farkon rayuwa da ilimi gyara sashe

Ya halarci makarantar firamare ta Kuki a shekarar 1978 sannan ya yi karamar sakandare a makarantar gwamnati da ke Rano (1983) sannan ya yi babbar sakandare a Kwalejin fasaha ta gwamnati, Bagauda (1983-1986). [1] Daga 1986-1990 ya yi kwas dinsa na N.C.E Technical a Kano State Polytechnic, School of Technology, Kano, kafin ya wuce Kwalejin Ilimi ta Tarayya, Kano (1995-1998) don kara ilimi.

Aiki da Siyasa gyara sashe

Ya yi aiki da ma'aikatar ilimi ta jiha daga 1991-2011. Ya samu matsayi har ya zama Principal. [2]

A shekarar 2011 ne aka fara zaɓen shi a matsayin dan majalisar dokokin jihar sannan aka sake zabe shi a shekarar 2015 a karo na biyu. Sannan Akaro na uku aka kara zabarshi a 2019.

Manazarta gyara sashe