Abinci na Tamil salon abincine na Mutanen Tamil wanda ya samo asaline daga kudancin Indiya na jihar Tamil Nadu da makwabciyar Sri Lanka . A lokuta na musamman, ana bada abincin gargajiya na Tamil a hanyar gargajiya, ta amfani da ganyen ayaba a maimakon kayan aiki. Bayancin abinci, ana amfani da ganyen ayaba a matsayin abinci na biyu ga shanu. Abincin karin kumallo na yau da kullun ya ƙunshi idli ko Dosas tare da chutney. Abincin rana ya haɗa da shinkafa, sambar, curd, kuzhambu, da kuma rasam.