Abimbola Windapo wani farfesa ne a Najeriya a fannin kula da gine-gine a Jami'ar Cape Town. Ita ce farfesa mace ta farko a fannin Gudanar da Gine-gine a Najeriya da Afirka ta Kudu.[1]

Abimbola Windapo
Rayuwa
Sana'a

Tarihin Rayuwa

gyara sashe

Windapo ta sauke karatu a jami'ar Ife a shekarar 1987 inda ta yi digiri a fannin gine-gine sannan ta wuce Jami'ar Lagos inda ta samu digiri na biyu a fannin gine-gine. Ta yi aiki da Bouygues Nigeria a matsayin injiniyan karatu da tsare-tsare. Ta koma Lagos State Polytechnic a shekarar 1996, sannan ta koma Jami’ar Legas a shekarar 1998. A lokacin tana Jami’ar Legas ta kammala digirin digirgir a fannin gine-gine a shekarar 2005. An nada ta a Jami’ar Cape Town a shekarar 2009 kuma ta samu karin girma a matsayin cikakkiyar Farfesa a shekarar 2020.[1][2]

Ta zama 'yar'uwar cibiyar gine-gine ta Najeriya a shekarar 2007.[1]

Ta karɓi lambar yabo ta 2020 ta South32 Award in the Engineering Research Capacity Development wanda Cibiyar Kimiyya da Fasaha ta Ƙasa ta gabatar.[3][4]

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 1.2 Carla, Bernado (2020-12-02). "SA and Nigeria's first woman professor in construction management". www.news.uct.ac.za (in Turanci). Retrieved 2021-07-01.
  2. Steed, Leila (2020-12-14). "First female construction professor in SA and Nigeria". KHL Group (in Turanci). Retrieved 2021-07-01.
  3. Forrest, Nicole (2021-06-17). "South Africa and Nigeria must join forces for Africa's future". www.news.uct.ac.za (in Turanci). Retrieved 2021-07-01.
  4. Krige, Nadia (2020-07-31). "UCT engineer awarded 'science Oscar' for capacity development". www.news.uct.ac.za (in Turanci). Retrieved 2021-07-01.