Dr. Abdulqadir Mohammed al-Baghdadi (1952 - August 2011, Tarhuna ) shi ne babban sakataren kwamitin jama'ar Libya a ƙarƙashin Muammar Gaddafi. Ya jagoranci hukumar mai da iskar gas da hukumar zuba jari ta Libiya. Ya kuma kasance shugaban mai kula da kwamitocin juyin juya hali. Yana daga cikin da'irar Gaddafi. [1] Bayan ɓarkewar yaƙin basasar Libya na farko, kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya sanya masa takunkumi .[2][3][1]

Abdulqadir al-Baghdadi
Rayuwa
Mutuwa ga Augusta, 2011
Sana'a
Sana'a Mai wanzar da zaman lafiya


Shi jami'i ne a ofishin jakadancin Libya da ke Landan a shekarar 1984, a lokacin an harbe WPC Yvonne Fletcher a wajen ofishin jakadancin.[4][5]

An tsinci gawarsa da harsashi a Tarhuna a cikin watan Agustan 2011 jim kaɗan bayan faɗuwar Tripoli .[6][5]

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 "Inside Gaddafi's inner circle". www.aljazeera.com (in Turanci). Retrieved 2023-02-11.
  2. "ABDULQADER MOHAMMED AL-BAGHDADI | United Nations Security Council". www.un.org. Retrieved 2023-02-11.
  3. "Isle of Man Government - Financial Sanctions: Libya". www.gov.im. Archived from the original on 2023-02-11. Retrieved 2023-02-11.
  4. Richard Hall (31 August 2011). "WPC Fletcher suspect 'killed in vendetta'". The Independent. Archived from the original on 2012-11-12.
  5. 5.0 5.1 Richard Spencer (30 August 2011). "Libyan 'behind Yvonne Fletcher's killing' found dead". The Daily Telegraph.
  6. Bowcott, Owen (2011-08-31). "Embassy murder suspect found dead". The Guardian (in Turanci). ISSN 0261-3077. Retrieved 2023-02-11.